Gwamnatin Yobe za ta gina gadar sama a kan N22.3bn
Published: 22nd, February 2025 GMT
Gwamnatin Jihar Yobe, ta rattaba hannu kan kwangilar gina gadar sama da titin ƙarƙashin ƙasa a tsakiyar garin Damaturu, Babban Birnin Jihar, kan kuɗi Naira biliyan 22.3.
Wannan wani mataki ne na ci gaba a ƙoƙarin gwamnatin samar wa al’umma ababen more rayuwa.
Sanata Katung ya damu kan yadda wasu ta’azzara ta’addanci a kudancin Kaduna Zaɓen ƙananan hukumomin Osun na nan daram – Gwamna AdelekeKwamishinan ayyuka na jihar, Injiniya Umar Duddaye ne, ya sanya hannu a madadin gwamnati, yayin da Injiniya Habib Geojea ya wakilci kamfanin da zai aiwatar da aikin, Messrs Triacta Nigeria Limited.
Kwamishinan ya bayyana cewa gwamnatin Mai Mala Buni na bai wa manyan ayyukan ci gaba fifiko, wanda ya haɗa da tituna, gadoji, da magudanun ruwa.
Ya ce aikin gadar sama da ke shatale-shatalen Damaturu za a kammala shi cikin watanni 12.
Haka nan, an rattaba hannu kan kwangilar gina titin Damaturu zuwa Gambir tsakanin gwamnatin Yobe da kamfanin Messrs Elegance Construction Nigeria Limited, wanda za a kammala cikin watanni tara.
Kwamishinan ya ƙara da cewa ana shirin gina sabbin tituna masu tsawon kilomita 23.5 da magudanan ruwa masu nisan kilomita 27 a Damaturu, tare da sake da gyara titunan da ake buƙata.
Aikin zai shiga mataki na biyu a shekarar 2025.
Manajan yanki naTriacta Nigeria Limited ya tabbatar da cewa za su gudanar da aikin cikin inganci da wa’adin da aka tsara.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Gadar Sama
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Filato ta dakatar da haƙar ma’adinai saboda matsalar tsaro
Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya bayar da umarnin dakatar haƙar ma’adanai a faɗin jihar daga ranar 21 ga watan Fabrairu, 2025.
Ya yanke wannan shawara ne saboda ayyukan haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida wanda ke da alaƙa da laifuka da suka shafi ta’addanci, satar mutane, da fataucin miyagun ƙwayoyi.
Najeriya ta taɓarɓare bayan mulkin IBB – Peter Obi Babban mai kai wa Bello Turji makamai ya shiga hannuHaka kuma, ya ce yawan baƙi da ke shiga yankunan da ake haƙar ma’adanai na ƙara haddasa matsalar tsaro.
“Akwai ƙaruwar ayyukan haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba, wanda ke haifar da matsalolin tsaro a sassa daban-daban na jihar.
“Haka kuma, yawan baƙin da ke shiga yankunan haƙar ma’adanai na ƙara yawan laifuka kamar ta’addanci, garkuwa da mutane, da fataucin miyagun ƙwayoyi,” in ji Gwamna Mutfwang.
Domin shawo kan wannan matsala, gwamnatin ta kafa kwamitin da zai binciki waɗanda ke da izinin haƙar ma’adanai da kuma ƙirƙirar tsarin kula da ayyukan haƙar.
Gwamnan ya ƙara da cewa za su yi aiki tare da Gwamnatin Tarayya domin tabbatar da tsare-tsaren doka da kuma inganta matakan tsaro.
“Za mu haɗa kai da Gwamnatin Tarayya domin bitar yadda ake sanya ido kan ayyukan haƙar ma’adanai.
“Haka kuma, za mu tabbatar da cewa kamfanonin haƙar suna bai wa al’umma gudunmawa,” in ji shi.
Gwamnan ya yi alƙawarin duba matsalar tsaro a yankunan da ake haƙar ma’adanai gaba ɗaya tare da tabbatar da cewa kamfanonin haƙar ma’adanai suna taimaka wa al’ummomin yankunan da suke aiki a cikinsu.