DRC : Kwamitin Tsaro Na MDD, Ya Yi Da Goyan Bayan Da Rwanda Ke Bai Wa ‘Yan Tawayen M23
Published: 22nd, February 2025 GMT
Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, a karon farko ya yi Allah-wadai da kasar Rwanda kan goyon bayan da take bai wa mayakan kungiyar M23 a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango (DRC).
Kwamitin ya kuma nemi ksar ta Rwanda da ta”gaggauta” janye sojojinta daga gabashin Jamhuriyar Demokuradiyyar Kwango.
Kudurin na ranar Juma’a “ya kuma yi kakkausar suka ga hare-haren da kuma ci gaban da kungiyar M23 ke ci gaba da yi a arewacin Kivu da Kivu ta Kudu tare da goyon bayan dakarun tsaron kasar ta Rwanda”.
A wani labarin kuma sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya yi kira da a tsagaita bude wuta nan take a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango yayin wata tattaunawa ta wayar tarho da shugaban Kenya William Ruto.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Amurka Tammy Bruce a wata sanarwa da ta fitar ta ce “Sun jaddada cewa babu wata hanyar soji da za ta magance rikicin, kuma sun yi kira da a tsagaita bude wuta cikin gaggawa.”
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
’Yan bindiga sun kashe jami’an tsaro 10, sun jikkata 14 a Zamfara
Aƙalla jami’an rundunar tsaron al’umma ta Zamfara (CPG) 10 ne, suka rasu, yayin da wasu 14 suka jikkata a wani hari da ’yan bindiga suka kai musu a yankin Anka da ke Jihar Zamfara.
Sun kai harin ne a ranar Asabar bayan da jami’an tsaro suka kai farmaki wani sansanin ’yan bindiga da ke dajin Bagega a ranar Juma’a da Asabar.
An shiga ruɗani yayin da Sanusi II da Bayero ke shirin hawan salla a Kano Ɗan sa-kai ya kashe matasa biyu a BornoA yayin farmakin, sun kashe ’yan bindiga da dama kuma sun kuɓutar da wasu mutanen da aka sace a sansanin wani ƙasurgumin shugaban ’yan bindiga, Alhaji Beti.
Wata majiya ta bayyana cewa jami’an tsaro sun kuma ƙone gidan wani shugaban ’yan bindigar mai suna Bellon Kaura, wanda lamarin da ya fusata su.
“Kurakuran da suka yi shi ne komawa ta hanyar da suka bi a lokacin farmakin farko,” in ji wani shugaba a yankin Anka.
“’Yan bindigar sun tsere daga sansaninsu amma sun shirya tarko, sun yi kwanton-ɓauna, kuma suka buɗe wuta bayan jin ƙarar baburan jami’an tsaron.”
Harin ya yi sanadin mutuwar jami’an tsaro bakwai daga Anka da kuma uku daga Talata Mafara.
Sunayen waɗanda suka rasu sun haɗa da Shehu Lawali, Murtala Mesin, Ubandawaki Moda, Muhammad Want, Haruna Kwanar Maje, Ibrahim Ware Ware, Yusuf Ware Ware, Rabi’u Barbara, Lawali Dan Hassi Jangebe, da Badamasi Gima.
An yi jana’izarsu a Anka a ranar Lahadi, inda Gwamna Dauda Lawal ya halarta, tare da ɗaukar alƙawarin ci gaba da goyon baya wajen yaƙi da ’yan bindiga a jihar.