HausaTv:
2025-03-25@00:15:15 GMT

Isra’ila-Hamas: Za’ayi Musayar Fursunonin Karshe Karkashin Yarjejeniyar Farko

Published: 22nd, February 2025 GMT

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas, ta ca zata saki ‘yan Isra’ila shida yau Asabar a matakin karshe na yarjejeniyar tsagaita wuta ta farko da ta cimma da Isar’ila.

An kuma tsara Isra’ila za ta saki fursunonin falasdinawa Falasdinawa 602 a wannan Asabar a musayar wacce ita ce ta bakwai tun cimma yarjejeniyar a ranar 19 ga watan Janairu tsakanin Isra’ila da Hamas.

Tun dai bayan cimma yarjejeniyar Hamas ta saki Isra’ilawa 22, a yayin da ita kuwa Isra’ila ta saki fursunonin Falasdinawa sama da 1,100.

A karshen matakin farko na yarjejeniyar tsagaita bude wuta, za a yi musayar fursunonin Falasdinawa 1,900 da aka yi garkuwa da ‘yan Isra’ila  su 33 da suka hada da matattu takwas.

Ana dai ci gaba da tattaunawa kan mataki na biyu na yarjejeniyar tsagaita wutar tsakanin bangarorin biyu a yayin da dukkansu ke zargin juna da keta yarjejeyar.

Shugaban ofishin yada labarai na gwamnati a Gaza ya sanar da cewa sau fiyesama da 350 Isra’ila ta keta yarjejeniyar tsagaita da Isra’ila ta cim ma a ranar 15 ga watan Janairu.

Tun bayan sanya hannu kan yarjejeniyar tsagaita wuta, sojojin Isra’ila sun kashe tare da raunata Falasdinawa da dama ta hanyar hare-hare ta sama da suka hada da jiragen yaki da jirage marasa matuka, da harbe-harbe kai tsaye.

Sauran laifukan sun hada da kutsen da Isra’ila ta yi a yankunan kan iyaka da ke gabashin Gaza.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: yarjejeniyar tsagaita Isra ila ta

এছাড়াও পড়ুন:

Iran da UAE sun kirayi Isra’ila da Amurka da su kawo karshen hare-harensu a Gaza da Yemen

Kasashen Iran da Hadaddiyar Daular Larabawa sun bayyana matukar damuwarsu kan yadda gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta sake dawo da yakin kisan kare dangi a zirin Gaza da kuma hare-haren da Amurka ke kaiwa kasar Yemen.

A wata tattaunawa ta wayar tarho a wannan Juma’a, ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi da takwaransa na UAE  Abdullah bin Zayed Al Nahyan, sun tattauna batutuwan da suka shafi yankin, musamman ma ayyukan wuce gona da iri na Isra’ila a Gaza da kuma hare-haren Amurka a Yemen.

Araghchi ya yi kakkausar suka kan kisan gillar da gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta yi wa daruruwan Falasdinawa  da ba su ji ba ba su gani ba tun daga ranar Talata, yana mai jaddada cewa yin hakan saba yarjejeniyar tsagaita bude wuta ne da aka rattaba hannu a kansa.

Ya kuma yi Allah wadai da hare-haren da sojojin Amurka ke ci gaba da kai wa kasar Yemen, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mata da kananan yara da dama, tare da lalata muhimman ababen more rayuwa na yankin, da kuma jefa mutane cikin kangin talauci da yunwa.

Araghchi ya kara da cewa, laifuffukan da gwamnatin yahudawan sahyoniya ke aikatawa a Gaza da kuma harin da Amurka ta kai kan kasar Yaman na bukatar daukar matakin gaggawa da hadin gwiwa daga kasashen yankin da kum akasashen musulmi, domin dakatar da wannan ta’addanci da ke  ci gaba da kawo rashin tsaro a duk fadin yankin gabas ta tsakiya.

A nasa bangaren, Ministan kasar UAE Abdullah bin Zayed ya bayyana matukar damuwarsa kan tabarbarewar al’amura a yankin, yana mai bayyana lamarin a matsayin abin damuwa matuka.

Ya jaddada bukatar ci gaba da tuntubar juna tsakanin kasashen yankin domin hana ci gaba da tabarbarewar zaman lafiya.

Rahotanni sun tabbatar da cewa sojojin Isra’ila sun zafafa kai hare-hare ta sama da kuma ta kasa a zirin Gaza tun daga ranar Talata, inda suke  kai hari kan wuraren zaman jama’a da hakan ya hada da wuraren da aka tsugunnar da dubban mutane da suka rasa muhallansu da kuma gidaje, gami da asibitoci, tare da hana duk wasu ayyuka na jin kai ko ceton jama’a ko kai daukin gaggawa.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Fursunoni 12 sun tsere bayan fasa gidan yari a Kogi
  • Duniya na ci gaba da yin tir da Isra’ila kan dawo da hare-harenta a Gaza
  • Babban Kusa A Kungiyar Hamas Salah Al-Bardawil Ya Yi Shahada
  • Isra’ila ta kashe wani mamba na ofishin siyasa na Hamas
  • Araghchi : Ya kamata Duniyar Musulmi ta dauki mataki mai karfi kan Isra’ila
  • Kao Kim Hourn: Ba Ta Hanyar ‘Siddabaru’ Kasar Sin Ta Cimma Nasarori A Fannin Ci Gaba Ba Sai Dai Ta Hanyar Aiki Tukuru Kuma Mai Dorewa
  • MDD da EU sun yi tir da wargaza yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza da Isra’ila ta yi
  • Falasdinawa 80,000 ne suka halarci sallar Juma’a a mako na uku na Ramadan a masallacin Al-Aqsa
  • Iran da UAE sun kirayi Isra’ila da Amurka da su kawo karshen hare-harensu a Gaza da Yemen
  • A cikin kwanaki 3 Falasdinawa 605 sun yi shahada a kisan kiyashin Isra’ila a Gaza