Aminiya:
2025-02-22@22:14:54 GMT

Sibil Difens ta cafke mutum 17 kan aikata sata a Yobe

Published: 22nd, February 2025 GMT

Hukumar Tsaron Farin Kaya ta Sibil Difens (NSCDC), a Jihar Yobe, ta kama wasu mutum 17 da ake zargi da satar kayayyakin lantarki, na’urorin sadarwa a jihar.

Kwamandan rundunar, AS Dandaura, ya tabbatar da kamen a Damaturu, Babban Birnin jihar, inda ya ce an gano wuraren ajiya uku da ake amfani da su don ɓoye kayan sata.

Dalilan ƙara kuɗin Jami’ar Gombe — Gwamna Inuwa Gwamnatin Filato ta dakatar da haƙar ma’adinai saboda matsalar tsaro

Ya bayyana cewa samamen da aka kai ya taimaka wajen gano wuraren ajiya guda uku—ɗaya a kusa da ofishin Hukumar Alhazai a Damaturu, na biyu a Duriya bayan sabuwar kasuwa, sai kuma na uku a Abbari bypass.

Dandaura ya ce an kama shugaban wata ƙungiyar dillalan kayayyakin bola a yankin, Aliyu Ajakuta, wanda ake zargi da jagorantar aikata satar.

Haka kuma, an cafke wasu da ake zargi da hannu a laifin, ciki har da Umar Sai’adu mai shekara 17, Mohammed Salisu mai shekara 25.

Sauran sun haɗa da Ali Adam mai shekara 18, Ibrahim Mohammed mai shekara 19, Mohammed Musa mai shekara 20, Abdulhamid Mohammed mai shekara 15 da Hassan Dauda mai shekara 18.

Sauran da aka kama sun haɗa da Alhassan Yakubu mai shekara 26, Mohammed Babagana mai shekara 29, Mohammed Bashiru mai shekara 18, Mohammed Bello mai shekara 17, Adamu Abdullahi Usman mai shekara 20, Mustapha Babagana mai shekara 23, Tijani Bako mai shekara 19, Bashiru Adam mai shekara 18 da Lawal Salisu mai shekara 19.

Hukumar ta bayyana cewa ta ƙwato kayayyaki masu yawa daga hannunsu, ciki har da na’urorin sadarwa, igiyoyi masu sulke, manyan karafunan titin, farantin sola, batura, da sauran kayayyaki.

Kwamandan ya jaddada cewa za a gurfanar da waɗanda ake zargi a gaban kotu bayan kammala bincike.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: zargi mai shekara 18 da ake zargi

এছাড়াও পড়ুন:

Hisbah ta rufe gidajen rawa a Katsina

Hukumar Hisbah ta rufe gidajen rawa da ke gudanar da harkokinsu a Jihar Katsina.

Hukumar ta umarci ɗaukacin masu gidajen rawa da ke gudanar da harkokinsu a cikin dare a faɗin jihar da su rufe.

Shugaban Hukumar, Dakta Aminu Usman ne ya bada umarnin tare da gargaɗin masu wuraren da matakin ya shafa.

Ya bayyana cewa ɗaukar matakin ya zama dole domin kare tarbiyya da dokokin addinin Islama da kuma barazanar tsaro a jihar.

Jami’an tsaron al’umma 6 sun mutu a artabu da ’yan bindiga a Sakkwato NAJERIYA A YAU: Tanadin Dokar Kasa Kan Kirkirar Gwamnatin Bibiya A Kano

Sanarwar da ya fitar ranar Laraba ta bayyana cewa tabbatar da tarbiyya da kare dokokin Musulunci sun zama wajibi.

Ya ci gaba da cewa, “za a ɗauki tsattsauran mataki kan duk masu kunne ƙashi, kuma ann riga an umarci jami’an tsaro da su tabbatar da bin wannan sabuwar doka.”

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Wani mutum ya yi wa agolarsa fyaɗe ta samu juna biyu
  • An haifi alade mai fuskar mutum a Philippines
  • Gwamnatin Yobe za ta gina gadar sama a kan N22.3bn
  • ’Yan sanda sun daƙile satar mutane, sun kama wasu 3 a Borno
  • Majalisar Dokokin Jihar Jigawa Ta Kaddamar Da Rangadi A Karamar Hukumar Jahun
  • Iran Ta Yi Tir Da Shugaban Hukumar IAEA Saboda Sanya Siyasa Da Daukan Bangare A Jawansa Na Baya Bayan Nan
  • Jihar Kano Ta Samar Da Wani Salo Na Bunkasa Ilmin Addinin Musulunci A Jihar
  • Hisbah ta rufe gidajen rawa a Katsina
  • Trump Na Amurka Ya Zargi Shugaban Kasar Ukiraniya Da Kama –Karya Da Kuma Rusa Kasarsa Ba Tare Da Wani Dalili Ba