Leadership News Hausa:
2025-02-22@21:38:55 GMT

An Kammala Taron Ƙungiyar AU Na 38 A Ƙasar Habasha

Published: 22nd, February 2025 GMT

An Kammala Taron Ƙungiyar AU Na 38 A Ƙasar Habasha

“Idan ba a dau matakin da ya dace akan abin da ke faruwa a DRC ba, al’amarin zai faskara. Ba batun fitar da takardar jawabin bayan taro ne kawai muke yi ba. Dole a biyo bayan hakan da wasu muhimman matakai ko tsare tsare da zasu tabbatar da cewa an gabatar da wadannan al’amura kan teburin shawara tare da nemo mafita irin wanda ya dace da Afurka don warware matsalolin Afurka.

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Taro

এছাড়াও পড়ুন:

Jihar Gombe na ƙarfafa haƙƙoƙin yara masu nakasa — Ƙungiyar JONAPWD

Ƙungiyar Masu Nakasa ta ƙasa reshen Jihar Gombe (JONAPWD), ƙarƙashin jagorancin Shugabanta kuma Sakataren Zartarwa na Hukumar Kula da Masu Nakasa ta Jihar, Dokta Isiyaku Adamu.

Ƙungiyar ta shirya taro na musamman tare da iyayen yara da suke fama da matsala irin ta nakasar jiki da kuma ta taɓin hankali.

NNPP ta rasa Ɗan Majalisa na farko da ya koma APC Harin ’Yan bindiga: Mun yi asarar shanu sama da miliyan 4 – Miyetti Allah

Wannan taron na musamman, wanda aka gudanar a ofishin JONAPWD da ke Gombe, ya zama wata muhimmiyar dama don tattauna matsaloli, musayar ƙwarewa da kuma ƙarfafa fafutuka don kare haƙƙoƙin yara masu fama da matsala irin ta nakasar jiki da kuma ta taɓin hankali.

A jawabinsa, Dokta Adamu ya bayyana cewa yara masu nakasar jiki da kuma ta taɓin hankali na fuskantar manyan ƙalubale wajen samun ilimi mai inganci, kiwon lafiya mai nagarta da kuma shiga cikin al’umma.

Ya ce, wannan nakasa ta hankali da ta jiki tana nufin yanayi da ke shafar fahimtar ƙwaƙwalwa wajen koyo da hulɗa da jama’a.

Sai dai, Dokta Adamu ya yi nuni da cewa idan aka ba wa waɗannan yara goyon baya mai kyau da fahimta, za su iya bunƙasa basirarsu su yi fice, kuma su bayar da gudummawa mai ma’ana ga ci gaban al’umma.

Dokta Adamu ya kuma yi bayani ga iyaye game da dokar masu nakasa ta Jihar Gombe da Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya rattaba wa hannu kwanan nan. Ya bayyana dokar a matsayin wata gagarumar nasara da za ta tabbatar da kariya, ƙarfafawa da haɗa yara masu nakasa tare da iyalansu cikin al’umma.

Daga cikin muhimman kudurorin taron, akwai ƙarfafa yaƙin wayar da kai don isar da saƙon zuwa ga iyaye da masu kula da yara masu nakasa. Wannan zai taimaka wajen ƙarfafawa al’umma fahimtar baiwa da basirar da yara masu nakasar jiki da kuma ta taɓin hankali ke da ita.

Hakazalika, Dokta Adamu ya nuna godiyarsa ga Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya saboda jajircewarsa wajen inganta rayuwar masu nakasa ta hanyar zartar da dokokin da suka dace.

“Muna matuƙar godiya ga jagorancin gwamna da kuma jajircewarsa wajen tabbatar da rayuwar masu nakasa ta inganta,” in ji shi.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Tarihin Shugaban Ƙasar Mali Na Farko Sundiata Keita (2)
  • Yake-Yaken Kasa Da Kasa Ne Suka Mamaye Taron G20 Na Ministocin Harkokin Wajen Kungiyar A Afirka Ta Kudu
  • Amurka Da Rasha Sun Kammala Tattaunawar Kawo Ƙarshen Yakin Yukiren A Ƙasar Saudiyya
  • Kallon-Kallo: Ƙungiyar Ƙwadago Da ‘Yan Nijeriya
  • Najeriya ta taɓarɓare bayan mulkin IBB – Obi
  • Nijar: Taron Kasa Ya Bukaci Sojoji Su Yi Mulkin Rikon Kwarya na Shekara 5
  • Saudiyya ta Gayyaci Kasashen Larabawa Kan Batun Kan Batun Gaza
  • Jihar Gombe na ƙarfafa haƙƙoƙin yara masu nakasa — Ƙungiyar JONAPWD
  • Turkiya Ta Karbi Bakuncin Tattaunawar Sulhu Tsakanin Habasha Da Somaliya