Aminiya:
2025-02-22@21:44:02 GMT

Ɗan Abacha ya kare mahaifinsa bayan ƙaddamar da littafin IBB

Published: 22nd, February 2025 GMT

Sadiq S. Abacha, ɗan Tsohon Shugaban Mulkin Soji na Najeriya, Janar Sani Abacha, ya bayyana mahaifinsa s matsayin mutum mai nagarta duk da sukar da ake yi masa har yanzu.

A wani rubutu da ya wallafa a shafukan sada zumunta, Sadiq, ya ce an jima ana cin amanar mahaifinsa, amma tarihi zai yanke masa hukunci ta hanyar yin adalci.

Sibil Difens ta cafke mutum 17 kan aikata sata a Yobe Dalilan ƙara kuɗin Jami’ar Gombe — Gwamna Inuwa

“Mutumin nan Abacha—kullum sukarsa da cin amanarsa kuke yi a asirce. Tarihi zai tuna ka a matsayin shugaba nagari, ko da kuwa sun ci gaba da ƙoƙarin rage maka ƙima.

“A matsayina na ɗanka, yau na fi alfahari da kai. Lallai kai ne mutumin da suke so sun zama ko da rabinka ne kuwa,” in ji shi.

Ya kammala rubutunsa da karin maganar Hausawa: “Duk wanda ya yi jifa a kasuwa…”

Rubutun nasa ya zo ne kwanaki kaɗan bayan tsohon shugaban mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida (IBB), ya ƙaddamar da littafinsa.

Littafin ya jawo cece-kuce sosai, musamman kan soke zaɓen ranar 12 ga watan Yunin 1993.

A cikin littafin, Babangida ya tabbatar da cewar MKO Abiola ne ya lashe zaɓen, amma ya ce wasu a cikin gwamnatinsa, musamman Abacha, suka tilasta masa soke sakamakon zaɓen.

Janar Sani Abacha ya mulki Najeriya daga 1993 zuwa lokacin rasuwarsa a 1998.

Wasu na yaba wa mulkinsa saboda gyaran tattalin arziƙi da tsaro, yayin da wasu ke sukarsa bisa cin hanci da take hakkin ɗan Adam.

A gefe guda kuma, Gumsu Abacha, ɗaya daga cikin ’ya’yan marigayin, ta mayar martani game da littafin da IBB ya ƙaddamar.

A wani saƙo gajere da ta wallafa a shafin X (Twitter), wanda ke kama da habaici.

Haka kuma, ta sake wallafa wasu rubuce-rubuce da ke cewa Babangida ya zargi Abacha da laifuka ne domin ba shi da ikon kare kansa.

Ga hotunan a ƙasa:

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: ya ya Kare Mahaifi

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamna Adeleke Ya Kaɗa Ƙuri’a a Zaɓen Ƙananan Hukumomin Osun

Gwamnan Jihar Osun, Sanata Ademola Adeleke, ya kaɗa ƙuri’arsa a zaɓen ƙananan hukumomi da aka gudanar a faɗin jihar a ranar Asabar. Gwamnan ya isa rumfar zaɓensa da ke Sagba/Abogunde, Ƙaramar Hukumar Ede, inda aka tantance shi kafin ya kaɗa kuri’arsa.

Zaɓen, wanda ake gudanarwa don zaɓen sabbin shugabanni a ƙananan hukumomi 30 na jihar, ya samu fitowar masu zaɓe sosai tare da ingantaccen tsaro. Gwamna Adeleke ya yaba da yadda zaɓen ke tafiya cikin lumana, inda ya buƙaci al’umma su ci gaba da kaɗa ƙuri’a ba tare da tsoro ko matsin lamba ba.

Gwamnan Shekarar 2024: Sanata Ademola Jackson Nurudeen Adeleke An Yanke Wa Mutane 5 Hukuncin Kisa Bayan Sun Kashe Wani Bafullatani A Jihar Osun

Da yake jawabi ga manema labarai bayan kaɗa ƙuri’arsa, ya jinjinawa hukumar zaɓe ta Jihar Osun (OSSIEC) bisa shirya ingantaccen zaɓe. Ya kuma jaddada muhimmancin dimokuraɗiyya a matakin ƙananan hukumomi, yana mai kira ga ‘yan jihar da su fito kwansu da kwarkwata domin amfani da hakkinsu na zaɓe.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Har Yanzu Mahaifina Abacha Ne Ya Tsone Musu Ido – Sadiq Abacha
  • Gwamna Adeleke Ya Kaɗa Ƙuri’a a Zaɓen Ƙananan Hukumomin Osun
  • Wasu sassan Abuja za su kasance cikin duhu a ƙarshen mako – TCN
  • Zaɓen ƙananan hukumomin Osun na nan daram – Gwamna Adeleke
  • Najeriya ta taɓarɓare bayan mulkin IBB – Obi
  • An tara Naira 16 a taron ƙaddamar da littafin IBB
  • Iran Ta Yi Tir Da Shugaban Hukumar IAEA Saboda Sanya Siyasa Da Daukan Bangare A Jawansa Na Baya Bayan Nan
  • Ba ni da hannu a kisan Dele Giwa — Janar Babangida
  • Na yi nadamar soke zaɓen 1993 — Babangida