Akwai Babban Aiki A Gabana, Cewar Amorim
Published: 22nd, February 2025 GMT
Premier League ranar Asabar 22 ga watan Fabrairu Eberton da Man United
Premier League ranar Laraba 26 ga watan Fabrairu Man United da Ipswich
English FA Cup ranar Lahadi 2 ga watan Maris Man United da Fulham.
.এছাড়াও পড়ুন:
An rufe Jami’ar Kogi saboda zanga-zangar ɗalibai
Hukumomin Jami’ar Tarayya da ke Lokoja a Jihar Kogi, sun rufe jami’ar har zuwa wani lokaci domin daƙile ci gaba da asarar rayuka da dukiya.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun magatakarda kuma sakatariyar majalisar Jami’ar, Dokta Rebecca Aimiohu Okojie, a ranar Alhamis kuma ta bayyanawa manema labarai a Lokoja.
Jihar Gombe na ƙarfafa haƙƙoƙin yara masu nakasa — Ƙungiyar JONAPWD NNPP ta rasa Ɗan Majalisa na farko da ya koma APCHukumar Jami’ar ta yi zargin cewa, ɗaliban sun tare babbar ƙofar shiga jami’ar ne tun bayan haɗarin da ya yi sanadin mutuwar ɗaliban jami’ar biyar a ranar Litinin, wanda ya sa shiga harabar jami’ar ke da wuya.
“Rufewar jami’ar ya biyo bayan asarar rayuka da ɗalibai biyar suka yi a wani mummunan haɗarin tirela a Felele, ranar Litinin 17 ga Fabrairu, 2025.
“Tun faruwar lamarin, ɗalibai sun tare ƙofar jami’ar duk da kakkausar murya daga gwamnatin jihar da kuma ƙoƙarin da hukumomin jami’ar suka yi na a kwantar da hankula.
“Saboda haka, bisa shawarar hukumomin tsaro na jihar da kuma daƙile ci gaba da asarar rayuka da dukiya, shugaban jami’ar bayan shawarwarin hukumar ta yanke, shawarar a madadin majalisar jami’ar cewa jami’ar, jami’ar da rassanta za a rufe su har sai baba-ta-gani. Ɗalibai za su bar wuraren karatu kafin ƙarfe 12 na rana ranar Alhamis, 20 ga Fabrairu.”