Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Alhassan (a) 20
Published: 22nd, February 2025 GMT
19-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa Shirin wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma ko cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane rastan na shahid Aya. Murtadha muttahhari, ko cikin littafin Mathnawi na maulana jalaluddeen, Rumi, ko kuma cikin wasu littafan.
///… Madalla, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, mun ci gaba da kawo maku sirar Imam Alhassan (s) Jikan manzon All..(s) sannan limami na 2 daga cikin limamai masu tsarki daga iyalan gidan manzon All..(s) kuma da, na farko ga Fitima(s) diyar manzon All..(s).
A cikin shirimmu na yau zamu dora daga inda muka tsaya a cikin shirimmu da ya gabata, inda muka bayyana yadda Imam Ali (s) ya kafawa wadanda suka kwace masa hakkinsa na khalifancin manzon All..(s) Hujjo masu karfi ta yadda na cewa hakkinsa ne aka kwace.
A lokacinda suka dabaibaye shi da igiyoyi suka fitar da shi daga gidansa, suka kawo shi gaban Khalifa a Abubakar, sannan Umar ya ce masa, ka yi bai’a! sai yace ba zai yi ba, don shi yi cancanta su yi masa bai’a. sai Abuubaida dan jarra ya zu kusa da shi ya fada masa cewa, wadannan dattawa ne daga cikinmutanenka, kai yaro ne, baka da tajruba, baka da kwarewanda da suke da shi. Sannan idan All..ya yi kana da nisan kwana, shugabanci naka ne. don ka cancanci hakan, saboda abinda ka gabatar …
A lokacin da ya kammala, sai Imam ya bashi hujjo na hankali wadanda ba wanda zai iya inkarinsu dangane da matsayin iayalan gidan manzon All..a cikin al-ummarsa.
Haka ma mun kawo kadan daga cikin hujjojin da Zahra (s) ta fada masu a gaban Khalifa na farko a cikin masallacin manzon All..(s). …
Daga karshe khalifa na farko ya bayyana cewa ba zai tilasta masa bai’a ba idan har ba zai yi ba.
Daga cikin hujjojin da, gaba dayansu wati Imam Ali da Fatimah da Alhassan da Alhussan (a) sun tabbatar hujja a kan dukkan musulmi a Madina, muhajirun da Ansar, suna shiga gida-gida, suna fada masu cewa wannan hakkinmu ne aka kwace ku taimaka mana mu dawo da hakkimmu: Sai su maida martani da cewa: Hakika mun rika mun yi wa wannan mutum bai’a. sai tace(s).
Wani lokacin kuma sai ta ce masu: Shin zaku bar gadon manzon All…ya fita daga gidansa ya koma gidan wani? Sai su kawo uzurinsu, suna cewa: Ya diyar manzon All..(s) da mijinki ya rika Abubakar zuwa garemu da bamu zabi waninsa ba.
Sannan Imam Ali (a) ya ce: Shin kuna ganin in bar manzon All..(s) bai sa shi a kabarinsa ba, in fito ina jayayya da wasu kan kujerar shugabancinsa?
Da haka suka zagaya gidajen mutanen Madina kakab ba su sami wadanda zasu taimaka masu ba don dawo da hakkinsu kwato hakkinsu.
Sai Zahrah(s). tana fada masu cewa: Baban Alhassan yayi abinda ya dace yayi. Su, sun aikata abinda All..zai yi masu hizabi a kansa.
Hakika Zahra (s) ta yi khuduba mai zafi don zaburar da mutane, su yi tawaye ga Abubakar, ta kodaitar da su, kan su yunkura don mayarwa Amirul muminin (S) Khalifanci.
Ta fada a cikin wata Khudubar ga kabilar Banu Qilah : Yaku Qilah, shin za’a kwace mani gadon mahaifina kuna gani, kuna ji, kuma kirata na isarku? Kuma sauti na yana isarku? Sannan kuna da yawa? …. Ku zababbun All…ne wanda ya zaba da alkhairinsa. … shin kun ya baya ne bayan da kun kasance a gaba, ? kun yu rauni ne bayan tsananinku, kun zama matsorata ne bayan jarunta daga yakar mutane wadanda suka karya alkawulansu? Sun kuma yi suka a cikin addininku, ku yaki shuwagabannin kafirci, lalle basa da rikon alkawali, mai yuwa zasu kawo karshen kafircin….}.
Hakikan ta kunnan wuyan bore, Sai dai Abubakar ya karbeta da neman uzuri, da kuma girmamawa, da lallabarta, har sai da kashe wutar boren da ta tayar, da haka kuma zukatan mutane suka lafa, don haka bata sami damar dawo da hakkin amirulmuminina daga Abubakar ba.
Sai kawai tana kai kukanta a gaban mahaifinta kan irin halin da ta sami kanta. Daga musibu da kuma cutarwa daga wasu daga cikin sahabban manzon All..(s).
Abinda ya tabbata a cikin zuciyar Amiruulmuminina (a) ya shiga cikin zuciyar dansa Imam Hassan (a), kuma yana masa zafi, sai wata rana ya je masallacin kakansa manzon All..(s) sai ya ga Abubakar yana khuduba, sai ya daka kansa ya dubi Abubakar sai ya ce masa, ka sauka daga mimbarin babana, ka je wajen mimbarin babanka.
Sai mutane suka juya faskokinsu bayan sun ji muryarsa, sai suka ga Imam Hassan Dan Aliyu dan Abitalib (a) yake magana. Sai Abubakar ya amsa masa da cewa ka fadi gaskiya-na rantse da All..Lalle mimbarin babanka ne, ba mimbarin babana ba.
Lalle hujjacewar Imam Hassan (a) da wadannan kalmomi yana yara, ya tabbatar mana yanda kwace hakkin mahaifinsa yake kona masa zuciyarsa. Har’ila yau yana cewa basu taba amincewa da khalifancin Abubakar ba, sai dai an fi karfinsu.
Imam Hassan (a) ya saba ganin kakansa manzon All..(s) yana khuduba a kan wannan mimbarin yana kiran mutane zuwa ga hanyar All..T, amma a halin yanzu wannan hasken ya babu shi.
Sai kuma Salman Alfarisi, babban sahabin manzon All..bafarise, wata rana ya fadawa Khalifa na farko, Yace: Ya Abubakar, zuwa ga wa kake maida al-amarinsa idan baka san wani abu ba?. Kuma ga wa kake fakewa idan an tambayeka abinda baka sani ba? Menen uzurinka na gabatar da kanka kan wanda ya fika ilmi? Kuma wanda ya fika kusanci da manzon All…(s), kuma wanda yafi ka sanin fassarar littafin All..mai girma da daukaka, da sunnar manzonsa (s)?. wanda annabi (s) ya gabatar da shi a rayuwarsa?, sannan yayi maku wasiya da riko da shi bayan mutuwarsa?, sai kuka yi watsi da zancensa, kuka manta da wasiyyarsa. Kuka sabawa wa’adinsa, kuka kwance alkawalinda kuka yi da shi, kuka kwance kullin da kuka yi da shi. Kullin nan da ya kulla shi a kanku, ? Na tafiya yaki tare da tutar Usama.?
Sai kuma hujjacewar Ammar dan Yasir ga Abubakar, mai tsarki dan tsarkakekke ya tashi yana fadar cewa: Ya ku Quraishawa, …ya musulmi,! Idan kun sani ! idan baku sani ba to ku sani, Lalle Iyalan gidan manzonku sun fi cancanta kuma suka fi zama masu hakkin gadon al-amarinsa.
Kuma su suka karfi a kiyaye addini, kuma sun fi aminci ga mumina, kuma su suka fi kowa kiyaye addinisa, kuma sun kowa iya nisiha ga al-ummarsa, ku umurci mutuminku ya mayar da hakki ga ma’abocinsa kafin igiyarku da shi yayi karfi. Al-amarinku yayi rauni, sannan sabani tsakaninku ya bayyana, sannan fitina a tsakaninku ta yi girma. Ku rarraba a tsakaninku, kuma makiyinku ya yi kodayin samun nasara a kanku, kuma hakiki kun san cewa Banu Hashim sun fi ku cancanta da wannan al-amarin.
Kuma Aliyu ya fi ku kusa da annabinku kanku, shi Aliyu a cikinsu (banu Hashim) shi ne mai jibantar al-amarinku a wajen All..da manzonsa (s).
Da kuma kun san bambanci a tsakaninku da shi a fili yake, daga lokaci zuwa lokaci, a lokacinda ya rufe kofofinku zuwa cikin masallaci sai kofarsa…
Masu sauraro a nan zamu dasa aya a cikin shirimmu nay au msai kuma wata fitowa idan All…ya kaimu wassalamu alaikum wa rhamatullahi wa barakatuhu.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: masu sauraro wadanda suka ga Abubakar
এছাড়াও পড়ুন: