Haɗarin mota ya laƙume rayuka 12 a Neja
Published: 22nd, February 2025 GMT
Aƙalla mutum 12 — ciki har da mata huɗu da maza takwas — sun riga mu gidan gaskiya a sanadiyyar wani mummunan haɗarin mota da ya auku a kan hanyar Lapai zuwa Agaie da ke Jihar Neja.
Wani da lamarin na safiyar wannan Asabar ɗin ya faru a kan idonsa, ya shaida wa Aminiya cewa uku daga cikin matan da suka rasu ’yan gida ɗaya ne.
Sai dai wasu fasinjoji uku da suka haɗa da mata biyu da direban motar sun tsallake rijiya da baya, inda a yanzu suke samun kulawa a Babban Asibitin Lapai.
Bayanai sun ce haɗarin ya auku ne bayan wata taho-mu-gama da aka yi tsakanin wata mota ƙirar bas ɗauke da fasinjoji 15 da kuma wata tirela a daidai ƙauyen Nami.
Da yake zantawa da Aminiya ta wayar tarho, direban motar, Mohammed Baba, ya ce lamarin ya auku ne a yayin da suke kan hanyar tafiya Ƙaramar Hukumar Katcha bayan sun taso daga tashar mota ta Kasuwar Gwari da ke birnin Minna.
Direban ya alaƙanta haɗarin da tsautsayi wanda ya ce ya auku ne yayin da direban tirelan ya yi yunƙurin ƙetare wata mota da ke gabansa, lamarin da ya janyo motocin suka yi karo da juna.
Sai dai ya ce tuni direban tirelan ya arce da bayan faruwar lamarin.
Kwamandan Hukumar Kiyaye Haɗura ta Ƙasa FRSC shiyyar Neja, Kumar Tsukwam, ya tabbatar da faruwar lamarin.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Haɗarin mota Jihar Neja
এছাড়াও পড়ুন:
Ba ni da hannu a kisan Dele Giwa — Janar Babangida
Tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida ta nesanta hannunsa da kisan gogaggen ɗan jarida kuma Babban Editan Jaridar Newawatch, Dele Giwa.
An kashe Dele Giwa wanda fitaccen mai sukar gwamnatin Babangida ne, ta hanyar wasikar bom a gidansa da ke Legas a ranar 19 ga watan Oktoban 1986.
Kwana biyu kafin kisan nasa wani babban jami’in Rundunar Leƙen Asiri ta Soji ya zargi Dele Giwa da yin fasa-kwaurin makamai da ƙasashen da nufin tayar da zaune tsaye a Najeriya
Sakamakon haka, dan jaridar ya yi hanzarin sanar da lauyansa, Gani Fawehinmi, game da halin da ake ciki.
Na yi nadamar soke zaɓen 1993 — Babangida NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Ba Za Mu Sauke Farashin Burodi Ba —’Yan kasuwaAmma bayan kwanan biyu, wani babban hafsan soji, Kamar Halilu Akilu, ya kira waya ta ba Dele Giwa tabbacin cewa kuskure aka samu kuma an gano ainihin lamarin, don haka ya kwantar da hankalinsa, komai ya wuce.
Wani abokin Dele Giwa a Newawatch mai suna Ray Ekpu, ya ce bayan ’yan sa’o’i ne aka kai wani sako gwamnati gidan Dele Giwa.
Ray Ekpu ya bayyana cewa ɗan Dele Giwa mai suna Billy ne ya karbi sakon mai ɗauke da tambarin Fadar Shugaban Ƙasar ya mika wa mahaifin nasa, wanda a lokacin yake cin abinci tare da wakilin Newawatch na London, Kayode Soyinka, wand ya kawo mishi ziyara.
Wasikar mai ɗauke da tambarin Fadar Shugaban Ƙasa na kuma dauke da rubutun “wanda aka aika wa kaɗai zai buɗe.”
Amma a yanzu shekara 41 bayan kisan na Dele, Janar Babangida ya nesanta hannunsa ko masaniyar lamarin.
Babangida ya nesanta kansa da lamarin ne a littafin Tarihi da da ya ƙaddamar a ranar Alhamis a Abuja.
Babangida ya bayyana fatan cewa wata rana gaskiya ta yi halintama gano hakikanin musabbabin mutuwar Dele Giwa.
Ya bayyana takaici cewa ’yan jarida sun kawo koma baya ga binciken kisan, inda suka yi saurin yanke hukunci kafin a kammala binciken.
A cewarsa, ya yi fatan a lokacin da gwamantin farar hula ta Olusegun Obasanjo ta sake buɗe binciken kisan Dele Giwa ’yan sanda za su samo sabbin hujjoji da ke nuna abin da ya faru, amma hakan bai samu ba.