Manufar ita ce a kawo karshen wannan tashin hankalin ta hanyar adalci, mai dorewa, wace dukkanin bangarorin da abin ya shafa za su aminta da ita” in ji Rubio ga menema labarai, duk da cewa babu jami’an Yukiren ko na Turai a wurin tattaunawar.

A wani labarin kuma, shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa ya shaida wa Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio cewa kasarsa ba za ta amince da korar Falasdinawa daga Gaza ba.

Mohammed bin Zayed Al Nahyan na mayar da martani ne ga shirin Shugaba Trump na Amurka na karbe ikon Zirin bayan sauya wa al’ummar Gaza matsuguni.

Shugaban na Hadaddiyar Daular Larabawa ya ce sake ginin Gaza abu ne da ya kamata a hada shi da shirin da zai samar da zaman lafiya.

A ci gaba da rangadin da Marco Rubio yake a Gabas ta Tsakiya tuni ya je Isra’ila da Sudiyya.

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Rasha

এছাড়াও পড়ুন:

Trump Yana Son Ganin Bayan Shugaban Kasar Ukraine Volodimir Zelezky Daga Kujerar Shugabancin Kasarsa

A dai-dai lokacinda shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bayyana a fili kan cewa baya son nganin tokwaransa na kasar Ukraine Volodimir Zelesky kan kujerar shugabancin kasarsa. Al-amura suna kara tabarbarewa a Kiev.

Jaridar Economist ta kasar Burtaniya ta bayyana cewa al-amarin ya bayyana kiri-kiri ne a lokacinda shugaban kasar Amurka ya zanta ta wayar tarho da shugaban kasar Rasha Vladimi Putin. Sannan aka gudanar da taro na farko tsakanin Amurka da Rasha a birnin riyad na kasar Saudiya ba tare da an gayyaci Zelesky ba haka ma, babu wani Jami’in tarayyar Turai da aka gayyata.

Jaridar ta nakalto wani babban jami’in gwamnati a Kiev yana cewa tun lokacinda suka fahinci cewa Trump baya son a ci gaba da yaki a Ukraine, sannan baya son shugaba Zeleski sun san haka zai faru.

Banda haka, Trump ya bayyana cewa Amurka ta kashe dalar Amurka miliyon 360 kan yakin da ta tabbatar da cewa Ukrain ba zata sami nasara ba. Banda wannan ya ji ta bakin Zeleski kansa kan cewa an sace rabin kudaden da Amurka ta bata.  A halin yanzu dai Trump ya bukaci a gudanar da zabe a kasar Ukraine, don ya tabbatar da cewa Zelesky bai da magoya baya da yawa. A cikin watan Fabrairun da mukr ciki ne yaki tsakanin Ukraine da Rasha yake cika shekaru 3 da fara shi.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Amurka Ta Ce Zata Gabatar Da Nata Shawara Dangane Da Kawo Karshen Yakin Ukraine Ga Babban Zauren MDD
  • An Kammala Taron Ƙungiyar AU Na 38 A Ƙasar Habasha
  • Shugabannin Kasashen Larabawa Sun Tattauna Kan Batun Gaza Da Yankin
  • Amurka Ta Bawa HKI Makami Mai Karfi, MK-87
  • Trump Yana Son Ganin Bayan Shugaban Kasar Ukraine Volodimir Zelezky Daga Kujerar Shugabancin Kasarsa
  • Jami’an Diblomasiyya Daga Kungiyar G20 Da Dama Sun Isa Afrika Ta Kudu
  • Babban Kwamandan IRGC Ya Bayyana Cewa: Amurka Da Isra’ila Ba Su Yi Nasara A Yakin Gaza Ba
  • Saudiyya ta Gayyaci Kasashen Larabawa Kan Batun Kan Batun Gaza
  • Turkiya Ta Karbi Bakuncin Tattaunawar Sulhu Tsakanin Habasha Da Somaliya