Jakadan Kasar Sin Ya Bukaci Dakatar Da Duk Wani Tashin Hankali A Gabashin Kongo
Published: 22nd, February 2025 GMT
Jakadan Kasar Sin Ya Bukaci Dakatar Da Duk Wani Tashin Hankali A Gabashin Kongo.
এছাড়াও পড়ুন:
DRC : Kwamitin Tsaro Na MDD, Ya Yi Da Goyan Bayan Da Rwanda Ke Bai Wa ‘Yan Tawayen M23
Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, a karon farko ya yi Allah-wadai da kasar Rwanda kan goyon bayan da take bai wa mayakan kungiyar M23 a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango (DRC).
Kwamitin ya kuma nemi ksar ta Rwanda da ta”gaggauta” janye sojojinta daga gabashin Jamhuriyar Demokuradiyyar Kwango.
Kudurin na ranar Juma’a “ya kuma yi kakkausar suka ga hare-haren da kuma ci gaban da kungiyar M23 ke ci gaba da yi a arewacin Kivu da Kivu ta Kudu tare da goyon bayan dakarun tsaron kasar ta Rwanda”.
A wani labarin kuma sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya yi kira da a tsagaita bude wuta nan take a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango yayin wata tattaunawa ta wayar tarho da shugaban Kenya William Ruto.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Amurka Tammy Bruce a wata sanarwa da ta fitar ta ce “Sun jaddada cewa babu wata hanyar soji da za ta magance rikicin, kuma sun yi kira da a tsagaita bude wuta cikin gaggawa.”