Hamas, Da OIC Sun Yi Allawadai Da Dirar Mikiyan Da HKI Take Yi A Tulkaram Na Yankin Yamma Da Kogin Joirdan
Published: 22nd, February 2025 GMT
Kungiyar Hamas wacce take iko da Gaza, a kasar Falasdinu da aka mamaye, ta yi allawadai da kutsawar da firai ministan HKI da kuma ministan yakin sa Israel Kantz zuwa cikin sansanin yan gudun hijira na Tulkaram a yankin yamma da kogin Jordan.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta kara da cewa sojojin HKI sun kutsa cikin sansanonin yan gudun hijira na Palasdinawa a Tulkaram da kuma Jenin tana rusa gidajen falasdinawa tana kuma kora da kuma kashe wadanda suka samu a cikin gidajen nasu.
A wani labarin kuma kungiyar kasashen musulmi ta OIC ta yi allawadai da rushe-rushen gidajen da gwamnatin HKI take yi a yankin yamma da kogin Jordan. Kungiyar ta yi kira da kasashen duniya su sa baki don dakatar da kashe Falasdinawa da kuma korarsu daga gidjensu da kuma rusa wasu gidajen.
Kungiyar ta kara da cewa kutsawa cikin sansanin yan gudun hijira na Tulkaram ci gaba da zaluncin da takewa Falasdinawa a tsawon shekaru 76 da suka gabata. Har’ila yau ministan harkokin wajen Falasdinawa ya yi tir da Natanyahu da kuma Kanzt kan abinda suke aikatawa a garin Tulkaram. Inda suke son korar faladinawa kimani 40000 da suke rayuwa a sansanin.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
UNRWA : hana shigar da kayan agaji Gaza, ya jefa yankin cikin matsanancin hali
Shugaban hukumar kula da ‘yan gudun hijira falasdinawa ta Majalisar Dinkin Duniya (UNRWA) ya yi gargadin cewa hana shigar da kayayyakin jin kai da Isra’ila ta yi a zirin Gaza ya jefa yankin cikin mawuyacin hali na rashin abinci.
“Makonni uku kenan da hukumomin Isra’ila suka hana shigar da kayayyaki cikin Gaza.
“Ba abinci, ba magani, ba ruwa, babu man fetur,” inji Philippe Lazzarini a cikin wani sako a shafukan sada zumunta.
Tun a ranar 4 ga watan Maris ne Isra’ila ta hana shigar da kayan agaji zuwa Gaza, bayan karewar kashi na farko na tsagaita bude wuta a yarjejeniyar da ta cimma da kungiyar gwagwarmayar falasdianwa ta Hamas data kunshi musayar fursunoni tsakanin bangarorin.
Lazzarini ya jaddada cewa al’ummar Gaza sun dogara ne kan shigo da kayayyaki daga yankunan da aka mamaye.
“Duk ranar da ta wuce ba tare da agajin jin kai ba, hakan na nufin yara da yawa suna kwana da yunwa, cututtuka na yaduwa,” in ji babban jami’in UNRWA.
Lazzarini ya bayyana haramcin taimakon a matsayin wani hukuncin bai daya ga al’ummar Gaza, wadanda akasarinsu kananan yara ne da mata.
Ya yi kira da a dage wannan kawanya da kuma kai agajin jin kai da kayayyakin kasuwanci zuwa Gaza.