Hamas Ta Mika Fursinonin HKI 6 Sannan Tana Dakon A Shiga Marhala Ta Biyu
Published: 22nd, February 2025 GMT
Kungiyar Hamas ta saki yahudawa 6 a marhala ta 7 na musayar fursinoni tsakaninta da HKI karo na 6 a yau Asabar.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar Falasdiawan na fadar cewa, bayan wannan musaya ta 7, suna dakon a fara marhala ta biyu na yarjeniyar da ke tsakaninta da HKI.
Labarin ya kara da cewa a wannan karon dakarun Hamas sun mika fursinonin yahudawan ne a garin Rafah na kan iyaka da kasar Masar.
Hamas ta bada sanarwan cewa firsononi Falasdinawa 50 wadanda aka yankewa hukuncin kisa, sannan 60 wadanda aka yankewa hukuncin mai tsawo, da 50 wadanda ake tsare da sub a tare da bayyana laifinsu ne HKI zata sake su a wannan musayar. Banda haka wasu 445 wadanda HKI take tsare da su a Gaza tun 7 ga watan Octoba ne za’a sallama.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Babban Kusa A Kungiyar Hamas Salah Al-Bardawil Ya Yi Shahada
Kungiyar gwagwarmayar Falastinawa ta Hamas ta fitar da wata sanarwa dangane da shahadar Salah al-Bardawil, mamba a ofishin siyasa na kungiyar kuma wakilin majalisar dokokin Falasdinu.
A rahoton tashar Al-Alam, bayanin Hamas yana cewa: Dr. Salah Al-Bardawil, wanda ya yi fice a fagen siyasa, kafofin watsa labarai, da fagage na kasa da kasa, kuma ake kallonsa a matsayin daya daga cikin manyan kusoshin Hamas, wanda yake a kan gaba wajen gwagwarmaya da sadaukarwa, ya yi shahada a kan tafarkin gaskiya.
Bayanin ya ci gaba da cewa: Bai taba gazawa wajen gudanar da ayyukansa na jihadi da hidima ga al’ummar Palastinu ba, ya kuma ci gaba da yin gwagwarmaya kan turba ta gaskiya da neman ‘yanci har zuwa karshen rayuwarsa.
Hamas ta jaddada cewa, jinin Dakta Al-Bardawil da matarsa da sauran shahidai wata fitila ce da za ta haskaka hanyar samun ‘yanci ga al’ummar Falastinu, kuma laifuffukan makiya ba za su taba raunana azama da jajircewar ‘yan gwagwarmaya a Falastinu ba.
A karshen wannan sanarwa da ta fitar a wannan Lahadi 23 ga Maris, 2025, kungiyar Hamas ta yi fatan samun rahama da aljannah ga Dr. Salah Bardawil da matarsa, tare da sauran wadanda suka yi shahada a kan tafarkin gaskiya.
Salah Al-Bardawil da matarsa sun yi shahada ne a daren ranar 23 ga watan Ramadan, bayan wani hari da yahudawan sahyuniya suka kai a kan tantin su da suke a yankin Al-Mawasi da ke yammacin birnin Khan Yunus.
Wannan harin dai wani bangare ne na kisan gilla da yahudawan Haramtacciyar Kasar Isra’ila suke ci gaba da yi kan al’ummar Gaza marasa kariya, tare da samun cikakken goyon baya da karfin gwiwa da dukkanin taimako kan hakan daga gwamnatin kasar Amurka.