Mataimakin Firaministan Sin Ya Zanta Da Sakataren Baitulmalin Amurka
Published: 22nd, February 2025 GMT
Jagoran kula da harkokin tattalin arziki da kasuwanci na kasashen Sin da Amurka a bangaren Sin, wanda kuma shi ne mataimakin firaministan kasar Sin, He Lifeng, ya zanta da sakataren baitulmalin Amurka, Scott Bessent, ta kafar bidiyo jiya Jumma’a 21 ga wata, inda suka yi musanyar ra’ayoyi kan wasu muhimman batutuwan da suka shafi tattalin arzikin kasashen biyu, bisa matsayar da shugabannin kasashen biyu suka cimma.
Bangarorin biyu duk sun amince da muhimmancin alakokin tattalin arziki da kasuwanci a tsakaninsu, inda suka yarda su ci gaba da tuntubar juna kan batutuwan da suka fi daukar hankulansu.
Har wa yau, kasar Sin ta nuna matukar damuwa kan matakin da Amurka ta dauka kwanan nan, na kara sanya wa hajojin kasar Sin harajin kwastam. (Murtala Zhang)
এছাড়াও পড়ুন:
Sin Ta Sanar Da Dokar Dakile Takunkuman Kasashen Waje
Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya sanya hannu kan dokar majalisar gudanarwar kasar Sin, mai kunshe da matakan dakile takunkuman kasashen waje ta janhuriyar jama’ar kasar Sin.
Tanadin dokar zai fara aiki ne tun daga ranar kaddamar da ita. Dokar ta tanadi matakai da aka inganta na dakile takunkumai daga kasashen waje, da tsararrun matakan mayar da martani, da karfafa tsarin gudanar da ayyuka masu nasaba, tsakanin ofisoshin sassan majalisar gudanarwar kasar Sin, da karfafa matakan aiwatar da sassan dokar. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp