PDP ta lashe zaɓen ƙananan hukumomin Osun
Published: 22nd, February 2025 GMT
Jam’iyyar PDP mai ci a Jihar Osun ta lashe zaɓen dukkan kujerun ƙananan hukumomi jihar guda 30 da na kansiloli 332 da aka gudanar yau Asabar.
Shugaban hukumar zaɓen jihar OSSIEC, Hashim Abioye ne ya sanar da sakamakon a wani taron ganawa da manema labarai da ya yi a jihar.
Wani mutum ya yi wa agolarsa fyaɗe ta samu juna biyu An haifi alade mai fuskar mutum a PhilippinesDa yake jawabi a yammacin wannan Asabar ɗin a birnin Osogbo, Hashim Abioye ya ce an samu nasarar gudanar da zaɓen bisa duk wasu tsare-tsare da dokoki suka tanadar.
Ya bayyana cewa jam’iyyu 18 ne suka shiga zaɓen domin cike giɓin da ake da shi a madafan iko na ƙananan hukumomin jihar guda 30.
Aminiya ta ruwaito cewa an samun takun saƙa tsakanin gwamnatin jihar da ’yan sanda da ma Ministan Shari’a na Nijeriya.
Ministan ya buƙaci a dakatar da zaɓen, sannan ’yan sanda suka ce sun samu bayanan sirri kan yiwuwar tayar da hargitsi, don haka suka yi kira ga gwamnan da ya dakatar da yunƙurinsa na gudanar da zaɓen, lamarin da shi kuma ya ce babu gudu, babu ja da baya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Jihar Osun Zaɓen Ƙananan Hukumomi
এছাড়াও পড়ুন:
Tsarin Fansho Na Jihar Jigawa Ya Yi Wa Sauran Jihohi Zarra- Premium Pension
Hukumar bayar da gudunmawar fansho ta Jihar Jigawa da Kananan Hukumomin jihar ta kulla yarjejeniyoyi da wasu mashahuran Hukumomin Asusun Fansho guda shida (PFA) da nufin tabbatar da tafiyar da kudaden fansho na jihar yadda ya kamata.
Shugaban ma’aikata na jiha Alhaji Muhammad K Dagaceri wanda ya jagoranci rattaba hannu kan yarjejeniyar a madadin gwamnatin jihar Jigawa a gidan fensho na Dutse ya ce taron yana kara jaddada kudirin gwamnati na tabbatar da gaskiya da inganci a tsarin tafiyar da fansho.
Ya kuma jaddada mahimmancin kula da harkokin kudi da kuma bukatar samar wa wadanda suka yi ritaya kudaden fansho domin ci gaba da gudanar da rayuwarsu.
“Wannan yarjejeniya ta nuna wani gagarumin ci gaba a kokarin da muke yi na ganin cewa ma’aikatanmu da suka yi ritaya sun samu haƙƙinsu a kan lokaci.”
Alhaji Muhammad Dagaceri ya ci gaba da bayyana cewa, an zabo shugabannin asusun fansho ne ta hanyar tantancewa.
A cewarsa, masu gudanar da ayyukan za su samar da ingantattun ayyukan gudanarwa, da suka hada da dabarun saka hannun jari, da kula da ayyukan asusu da inganta ayyukan abokan ciniki.
Shugaban Ma’aikatan ya ce Hukumar Fansho ta Jihar Jigawa za ta sa ido a kan hadakar, tare da tabbatar da cewa PFA sun bi ka’ida da kuma cika alkawuran da suka dauka ga Jihar da masu karbar fansho.
Ya jaddada sadaukarwar gwamnatin Gwamna Umar Namadi wajen kyautata jin dadin ma’aikatan da suka yi ritaya, yana mai cewa wannan wani bangare ne na kokarin inganta ayyukan gwamnati da kuma kaucewa rikon sakainar kashi a harkokin tafiyar da dukiyar jihar.
Da yake jawabi a madadin hukumomin na PFA Manajan Daraktan Asusun Fansho na Premium Hamisu Bala Idris, ya tabbatar wa hukumar cewa PFA da aka zaba za su ci gaba da aiki yadda ya kamata ta hanyar bin duk wasu sharuddan da ke cikin yarjejeniyar.
Hamisu, ya bayyana tsarin fansho na jihar Jigawa a matsayin wanda ya fi kowanne a fadin kasar nan.
A nasa jawabin, Shugaban Hukumar Fansho ta Jihar Jigawa da Kananan Hukumomi, Dokta Bilyaminu Shitu Aminu ya bayyana cewa, zababbun asusun fansho guda shida da za su kula da dukiyar hukumar su ne, Premium Pension Fund (Lead PFA), da PAL Pension, da GT Pension, da NLPC Pension, da Norrenberger Pension da Cruder.
Dakta Bilyaminu Shitu Aminu ya yabawa Gwamna Malam Umar Namadi bisa gagarumin goyon bayan da ya bayar ga shirin da ya sa Jihar ta zama abin koyi a kasar nan.
Usman Muhammad Zaria