Zan Samar da Karin Makarantu a Zaria – Dr. Abbas Tajuddeen
Published: 23rd, February 2025 GMT
Shugaban majalisar wakilai, Dr Abbas Tajuddeen ya bayyana aniyar kafa karin makarantu a Zaria.
Shugaban majalisar wakilai, Dr Abbas Tajuddeen ya ce za a kafa karin makarantu a mazabar tarayya ta zaria a kasafin kudin shekarar 2026.
Shugaban majalisar ya bayyana haka ne lokacin babban taron shekara karo na 31 da 32 na kungiyar bunkasa ilimi ta zaria, watau ZEDA da aka gudanar a Zaria.
Ya bayyana cewa makarantun da ake shirin kafa wa sun hada da makarantar firamare da sakandare na yara masu bukata ta musamman da kwalejin tarayya na koyon aikin noma da kiwo.
Shugaban majalisar ya kuma bayyana fara bada tallafi na musamman ga dalibin da ya fi kowa kwazo a fannin koyon ilimin kwamfuta da kuma dalibin da ya fi kowa nuna hazaka a bangaren makarantun sakandare dake lardin zazzau.
Abbas Tajuddeen bayan ya nuna rashin jin dadin sa bisa jinkirin da aka samu wajen biyan dalibai su 2500 kudin tallafin karatu da suke lardin zazzau,ya kuma bayyana kara yawan daliban zuwa 3000 a shekarar 2025.
Shugaban majalisar ya dora alhakin jinkirin da aka samu wajen biyan tallafin akan kaddamar da kasafin kudin shekarar 2024 inda ya bayyana cewa za a biya kudin da zarar al’amura sun daidaita.
Haka kuma ya bada sanarwar cewa zai gina wa kungiyar zeda tare da sanya kayayyaki irin na zamani a dakin taro da zai dauki kimanin mutane dubu daya.
Shugaban majalisar ta wakilai ya kara da cewa kudurin majalisar ne ganin ta bunkasa ilimi a matakin farko da inganta ilimin sakandare da na kimiyya da kawo sauyi a fannonin kirkira.
Domin haka a cewar sa zai magance matsalolin da ake fuskanta da kuma mai tasowa.
A don haka sai ya bukaci kungiyar da ta bullo da wani tsari da zai samar da yanayin baiwa malaman horo da shigar da iyaye cikin harkokin tattauna batutuwan da suka shafi ilimi.
Tun farko a jawabin sa na maraba,shugaban kwamitin tsare-tsare na kungiyar ta ZEDA, Dr Abdul Alimi Bello ya ce Kungiyar ta sami gagarumar nasara da ya nuna aniyar ta na samar da ingantaccen ilimi da bunkasa al’umma.
Ya ce cikin shekaru da dama, kungiyar ta kasance jagoran kungiyoyi masu zaman kansu a lardin zazzau da suke kula da ilimin zamani da bunkasa sana’o’in hannu.
A nashi jawabin, mai martaba Sarkin zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli ya bukaci kungiyar da ta yi amfani da kudaden shigar ta wajen tabbatar da samar da kyakkyawar sauyi a bangaren ilimi.
Haliru Hamza
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Makarabtu Zaria Shugaban majalisar
এছাড়াও পড়ুন:
Ko Raunin ‘Yan Wasa Zai Rage Wa Barcelona Karsashi A Kakar Bana?
Gwaje-gwajen da aka yi a ranar 17 ga Maris sun nuna cewa dan wasan tawagar farko Marc Casadó yana da rauni a gefen damansa, za a kara yin gwajin dan wasan don sanin girman raunin da kuma kwanakin da zai shafe ta na jinya, hakazalika Gwaje-gwaje a wannan rana kuma sun tabbatar da cewa dan wasan bayan kungiyar Iñigo Martinez yana da kumburi a gwiwarsa ta dama, za a yi wa dan wasan magani a Barcelona karkashin kulawar ma’aikatan lafiya na kungiyar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp