Leadership News Hausa:
2025-02-23@11:56:59 GMT

Na Fi Ɗaukar Noma A Matsayin Sana’a Fiye Da Waƙa -Rarara

Published: 23rd, February 2025 GMT

Na Fi Ɗaukar Noma A Matsayin Sana’a Fiye Da Waƙa -Rarara

Dauda ya kara da cewa, babu wata waka da zai yi ba tare da an bukaci ya yi ta don isar da wani sako ba. Haka zalika, Shugaba Tinubu, ba shi da wani buri na tara dukiya a halin yanzu; illa kawai dai fatan barin tarihi mai kyau a matsayinsa na Shugaban kasa, kamar yadda sauran mazan jiya; irin su Sir Ahmadu Bello da Abubakar Tafawa Balewa suka bari.

Dangane da abin da wasu ke dauka cewa, ana biyana makudan kudade; don yin wakokin da za su kawar da hankalin mutane, su sani cewa; na fi mayar da hankali a kan noma fiye da yadda nake yi wa harkar waka, dalili kuwa; ni manomi ne wanda a yanzu haka duk fadin yankin da nake, babu wani mai yin noma kamar ni.

Yanzu haka, ina noma a gona mai fadin Eka fiye da 100, sannan kuma; ina sa ran samun karin wata gonar mai girman Eka 500 da zan kara a kan wadda nake nomawa yanzu. Don haka, har Dam na sa aka yi min a cikin gonata, saboda noman rani; don haka kashi 70 na kudin shiga da nake samu yanzu, ya fito ne daga harkar noma, ba waka kamar yadda wasu ke tunani ba.

Daga karshe, mawakin ya ce; babu abin da yake jin dadi idan ya aikata, fiye da taimakon gajiyayyu, “Ina matukar jin dadi idan na taimaka wa wadanda ke bukatar taimako, domin abin da na yarda da shi shi ne, muddin ka taimaki wani; shi ma zai taimaki wani, daga karshe za a rasa wani wanda zai bukaci taimako a cikin mutane”, in ji Rarara.

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Waka

এছাড়াও পড়ুন:

Har Yanzu Mahaifina Abacha Ne Ya Tsone Musu Ido – Sadiq Abacha

Wannan bayanin da Babangida ya yi a kan zaɓen ya haifar da maganganu a kan irin rawar da Abacha ya taka wajen soke zaɓen da yadda ya hana Nijeriya komawa mulkin dimokuraɗiyya a wancan lokacin.

Marigayi Sani Abacha dai ya yi mulkin soja a Nijeriya daga shekara ta 1993 zuwa 1998 da ya rasu.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamna Namadi Ya Bayyana Karfafa Matasa A Matsayin Jigon Ayyukan Gwamnatinsa
  • Har Yanzu Mahaifina Abacha Ne Ya Tsone Musu Ido – Sadiq Abacha
  • Wani mutum ya yi wa agolarsa fyaɗe ta samu juna biyu
  • Kungiyar Hizbullah Ta Lebanon Ta Jaddada Rashin Amincewarta Da Mika Kan Kasar Ga Amurka Da Haramtacciyar Kasar Isra’ila
  • Masu Sana’ar Kamun Kifi Sun Koka Kan Ƙarancin Kuɗaɗen Shiga A Taraba
  • Babu Wani Abin Burgewa A APC, Za Mu Kori Wannan Gwamnati A 2027 – Tambuwal
  • Dakarun Kai Daukin Gaggawa Sun Kashe Mutane Fiye Da 400 A Yankin Al-Qatana Da Ke Jihar White Nile Ta Sudan
  • Yanzu-yanzu: Gini Ya Rufta Wa Ɗaliban GGTC Potiskum
  • An haramta wa manyan tireloli aiki a Najeriya