Sojojin Sudan Sun Tsananta Kai Hare-Hare Kan ‘Ya Tawayen Rapid Support Forces
Published: 23rd, February 2025 GMT
Sojojin Sudan na ci gaba da gudanar da ayyukansu na kai farmakin karshe da nufin murkushe ‘yan tawayen Dakarun Kai Daukin Gaggawa
Sojojin Sudan sun fara aikin wanzar da tsaro a wasu yankuna a jihar Al-jazira da ke tsakiyar kasar Sudan, tare da kara tsaurara matakan killace fadar shugaban kasar da ke karkashin ikon dakarun kungiyar Rapid Support Forces, wadanda a halin yanzu mayakan ‘yan tawayen suke fama da karancin kayayyakin aiki.
Sojojin Sudan sun kai farmaki kan dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces da ke kusa da gadar Soba, wadda ta hada kudancin Khartoum da gabashin Nilu a kan hanyar kogin Blue Nile, inda suka kwace iko da sansanonin dakarun ‘yan tawayen. A yayin da Dakarun kai daukin gaggawa suka yi ruwan bama-bamai a yankuna da dama na Gabashin Nile da Umm Dom a birnin Khartoum, inda suka kashe fararen hula 7 tare da jikkata wasu da dama.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Amnesty Ta Zargi Rundunar “RSF” Ta Sudan Da Cin Zarafin Mata
Kungiyar kare hakkin bil’adama ta kasa da kasa ” Amnesty International” ta bayyana cewa, rundunar kai daukin gaggawa ta “RSF” ta bautar da mata da kuma cin zarafinsu.
Kungiyar ta yi tir da abinda rundunar ta “RSF” ta yi akan mata da su ka manyanta da kuma ‘yan mata a tsawon lokacin yakin na Sudan da har yanzu bai zo karshe ba.
Wani sashe na rahoton kungiyar ya yi ishara da yadda wannan rundunar da take fada da sojojin kasar Sudan ta tarwatsa mutane daga gidaje da matsugunansu a fadin kasar.
Ita kuwa Hukumar dake kula da ‘yan gudun hijira ta MDD ( UNHCR) cewa ta yi da akwai yan kasar ta Sudan fiye da 100,000 da suke neman yin hijira zuwa kasashen turai a cikin wannan shekara ta 2025 kadai, tare da kara da cewa mutanen suna kara yanke kauna da samun wata mafita a cikin kasar, saboda raguwar agaji.
A cikin birnin Khartum da sojojin su ka kori dakarun na “RSF” an sami komawar mutanen da su ka yi hijira kamar yadda hukumar ta ( UNHCR) ta ambata.
Shugabar hukumar mai kula da ‘yan hijira ta MDD Olga Sarado wace ta gudanar da taron manema labaru a birnin Geneva ta bayyana cewa; Da akwai ‘yan Sudan su 484 da su ka isa cikin kasashen turai daga watan Janairu zuwa yanzu, da hakan yake nuni da samun Karin masu hijirar zuwa turai da kaso38%.
Ta kuma kara da cewa, matukar ba a kai wa kasar kayan agaji, to kuma masu yin hijira zuwa turai din zai karu.