Za A Fara Amfani Da Fasahar Tantance Satar Gida A Ingila
Published: 23rd, February 2025 GMT
Hukumomin da ke kula da wasannin kwallon kafa a kasar Ingila sun fara shirin fara amfani da fasahar tantance satar gida a karon farko a gasar cin kofin FA ta Ingila. A ranar Alhamis hukumar kwallon kafa ta Ingila ta sanar da cewa za a yi amfani da fasahar a wasanni bakwai da za a fafata a filayen kungiyoyin gasar Premier kuma hukumar FA ta ce nan gaba za a yi amfani da fasahar a wasannin gasar Premier.
Tun da farko kungiyoyin Premier sun amince da a soma amfani da fasahar a kakar wasa ta 2024 zuwa 25 amma aka jinkirta domin kammala gwaji kuma a kakar wasa ta 2022 zuwa 2023 ne hukumar kwallon Turai ta UEFA ta soma amfani da fasahar a wasannin gasar zakarun Turai. Hukumar FA ta ce fasahar za ta taimaka wajen tabbatar da tantance satar gida ta hanyar samar da hoto.
Yadda Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa Ta Gudanar Da Tantance Sabbin Kwamishinoni Amurka Ba Za Ta Cimma Burinta Bisa Matakin Kara Harajin Kwastam Kan Ma’adanan Karfe Da Goran Ruwa BaKuma a cewar hukumar, fasahar ba za ta ci karo da alkalanci ba amma za ta kara tabbatar da saurin tantance satar gida a wasanni sannan za a kuma yi amfani da fasahar bidiyo da ke taimaka wa alkalin wasa a wasanni takwas na gasar FA. A ranar Asabar 1 ga Maris ne za a buga wasannin FA zagaye na biyar wanda idan an kammala gasar wannan shekarar sabuwar fasahar za ta fara aiki nan take.
কীওয়ার্ড: a amfani da fasahar amfani da fasahar a
এছাড়াও পড়ুন:
An yi wa Jakadan Afirka ta Kudu da Amurka ta kora tarbar Jamurumai bayan komawarsa gida
Ebrahim Rasool, jakadan Afirka ta Kudu da gwamnatin Trump ta kora, ya samu tarba a wannan Lahadin daga daruruwan magoya bayansa da suke rera wakoki domin karrama shi a filin jirgin sama na Cape Town.
Jama’a sun kewaye Rasool da matarsa Rosieda bayan isowarsu, yayin da ‘yan sanda suka yi musu rakiya har zuwa tashar jirgin kasa.
Da yake yiwa magoya bayansa jawabi, Rasool ya ce, Abin da ya faru yana a matsayin wulakanta ku ne ku al’ummar Afirka ta kudu, amma kuma idan kuka tsaya tsayin daka kan manufofinku na ‘yancin kai to za ku ci gaba da rayuwa a cikin mutunci da daukaka.
Ya ce ba laifi muka yi ba, ammam kuma mun dawo gida ba tare da nadama ba.
Gwamnatin Trump ta kori Rasool sakamakon kalaman da ya yi a cikin shafukan yanar gizo, wanda gwamnatin Trump ke kallon kalamansa a matsayin batunci ga Amurka.
Korar Rasool, wanda tsohon mai fafutukar yaki da wariyar launin fata ne, ya kara dagula dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu, wadanda manufofin Trump na baya-bayan nan suka kara kawo tankiya da zaman doya da manja a tsakaninsu.