Mai Pataskum ya buɗe masallacin garin Danga a Yobe
Published: 23rd, February 2025 GMT
Mai martaba Mai Pataskum, Alhaji Umaru Bubaram Ibn Wuriwa Bauya, ya jagoranci bikin buɗe sabon masallacin Juma’a da aka gina a Garin Danga a Ƙaramar Hukumar Potiskum da ke Jihar Yobe.
Bikin kaddamar da sabon masallacin Juma’ar, wanda ya jawo shugabannin al’umma, malaman addini, da mazauna yankin ya nuna irin gagarumin ci gaba da aka samu a harkokin addinin musulunci a yankin.
Mai Pataskum, wanda ya yi fice wajen bayar da gudunmawa wajen samar da zaman lafiya da ci gaba a yankin, ya yaba da kokarin da masu bayar da tallafi na kasar Malaysia suka yi na gina masallacin, tare da jaddada rawar da yake takawa wajen samar da haɗin kai da ci gaban yankinbmasarautar.
Mai martaba Sarkin ya yi addu’ar fatan alheri ga al’ummar masarautar, jihar Yobe da ma kasa baki ɗaya.
Ya kuma yaba wa yadda kasar ta Malaysia ke taka rawar gani wajen ciyar da addinin musulunci gaba a faɗin duniya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Jihar Yobe
এছাড়াও পড়ুন:
Shirin Rigakafin Cututtuka Na UNICEF/GAVI Ya Sami Cikakken Hadin Kan Gwamnatin Jihar Jigawa
Gwamnatin jihar Jigawa ta yi alkawarin ci gaba da gudanar da ayyukan kiwon lafiya da aka gudanar karkashin hadin gwiwarta da Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF), da shirin samar da rigakafin cututtuka a kasashe masu tasowa(GAVI) a cikin shekaru uku da suka gabata.
Haɗin gwiwar wanda aka fara shi da yarjejeniyar fahimtar juna da aka rattaba hannu a shekarar 2022, an yi shi ne don haɓaka tsarin bada lafiya na jihar, da inganta tsarin rigakafi ta hanyar samar da kayan aiki da wadatattun ma’aikatan lafiya.
A wajen mika kayan aikin da aka gudanar a gidan gwamnati dake Dutse, Gwamna Umar Namadi ya ce shirin ya bayar da gudunmawa musamman wajen samar da inshorar lafiya na musamman ga mutane sama da dubu 143 a kananan hukumomi 27 na jihar.
Namadi wanda ya samu wakilcin mataimakinsa Injiniya Aminu Usman, ya ce manufofin yarjejeniyar sun yi daidai da ajandar gwamnatin jihar 12, wanda ya bai wa fannin lafiya fifiko ta hanyar sauya cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko tun daga tushe.
Mataimakin gwamnan wanda ya karbi tawagar UNICEF/GAVI karkashin jagorancin shugaban hukumar ta UNICEF a Najeriya, Dr Shyam Sharan-Pathak, ya ce gwamnatin za ta ci gaba da bullo da tsare-tsare don bunkasa harkar kiwon lafiya a fadin jihar.
Shi ma da yake jawabi, Kwamishinan Lafiya na Jihar, Dr Muhammed Abdullahi Kainuwa, ya ce aikin ya samu gagarumar nasara a tsawon wannan lokaci.
Ya ce an samu ingantacciyar hanyar adana alluran rigakafin, ta hanyar sayen kayayyakin adana sanyi na tafi da gidanka, da na’urorin sarrafa hasken rana kai tsaye.
Hakazalika Dakta Kainuwa ya ce, an samar da motoci 3 da suka rarraba kayayyakin aiki, sannan an dauki mutane 330 aiki.
Ya yabawa shugabannin addini da na gargajiya a jihar, bisa goyon bayan da suka bayar wajen wayar da kan jama’a a tsawon shekaru 3 da aka yi aikin.
A nasa jawabin babban sakataren ma’aikatar lafiya ta jihar Dr Kabiru Ibrahim, ya yabawa gwamna Namadi bisa jajircewarsa.
Dr Kabiru, ya lura cewa, kudurin gwamnatin na bin ka’idoji da manufofin ma’aikatar lafiya ta tarayya abin yabawa ne matuka.
Shi ma da yake nasa jawabin, babban sakataren hukumar kula da lafiya matakin farko na jihar, Dokta Shehu Sambo, ya ce yarjejeniyar ta jawo sabbin dokoki da suka shafi kiwon lafiya a jihar.
Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa, shirin karfafa tsarin kula da lafiya a matakin farko shiri ne na hadin gwiwa na tsawon shekaru 3 (wato daga shekarar2022 zuwa watan Maris na 2025) tsakanin GAVI da jihohi 8 na Najeriya wanda jihar Jigawa na daga cikinsu.
Usman Muhammad Zaria