Leadership News Hausa:
2025-02-23@16:34:01 GMT

Ministan Yaɗa Labarai Ya Taya Gwamna Bago Murnar Cika Shekara 51

Published: 23rd, February 2025 GMT

Ministan Yaɗa Labarai Ya Taya Gwamna Bago Murnar Cika Shekara 51

“Jajircewar sa ga haɓaka ababen more rayuwa, noma da ƙarfafa matasa yana ci gaba da mayar da Jihar Neja abin koyi wajen cigaba da wadata.”

 

Ministan ya ce yana taya gwamnan na jihar su murna, yana mai bayyana shi a matsayin jagora mai kishin hidimta wa al’umma da cigaban ƙasa.

 

Idris ya ƙara da cewa, “Yayin da yake bikin wannan rana ta musamman, ina taya shi murna a matsayin jagora wanda jajircewar sa ga hidima da shugabanci ke nuna ainihin cigaba.

 

“Ina roƙon Allah ya ci gaba da ba shi lafiya, hikima da ƙarfi don ya ci gaba da tafiyar da Jihar Neja zuwa matakai mafi girma.”

 

Ya kammala da taya Gwamna Bago murna, inda ya ce, “A karo na biyu, muna taya ka murna da fatan alheri a wannan rana mai albarka, Mai Girma Gwamna!”

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

MDD Ta CE Sake Tada Komatsar Tattalin Arzikin Kasar Siriya Zau Dauki Shekaru 50 Nan Gaba

MDD ta bada sanarwan cewa tattalin arzikin kasar Siriya na bukatar shekaru 50 nan gaba kafin ta koma kamar yadda take kafin yakin basasa a kasar.

Tashar talabijan ta Presstv ta nakalato shugaban hukumar UNDP Achim Steiner yana fadar haka a jiya Alhamis, ta kuma kara da cewa hukumar ta ta gudanar da bincike kuma ta gano cewa, rikici da yakin basasa da kuma mamayar kasar da sojojin kasashen yamma suka yiwa kasar, ya sa al-amura sun lalace a kasar, ta yadda idan tana bukatar komawa matsayinta kafin shekara ta 2011 tana bukatar rabin karni kafin hakan ya samu. Wato kasar Siriya ba zata koma kamar yadda take a shekara ta 2011 ba sai nan da shekara 2080.

Tace Siriya tana bukatar zuba jari mai yawa a ko wace shekara kafin ta sami wannan ci gaban. A halin yanzu dai kasha 90% na mutanen kasar Siriya suna rayuwan talaka. Sannan kasha 50% daga cikinsu basa da aikin yi. Sannan tattalin arzikin kasar GDP na kasar yana rabin matsayinsa a shekara ta 2011. Banda tallafi daga kasashen waje kasar Siriya tana bukatar zuba jari mai yawa don komawa kamar yadda take.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ministan Wajen Sin Ya Yi Kiran Hadin Gwiwar Kasashen G20 Don Gina Duniya Mai Adalci Da Ci Gaba Na Bai-daya
  • Gwamna Namadi Ya Bayyana Karfafa Matasa A Matsayin Jigon Ayyukan Gwamnatinsa
  • Sojojin Gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra’ila Suna Ci Gaba Da Luguden Wuta Kan Gabar Yammacin Kogin Jordan
  • Da Ɗumi-ɗumi: Sanata Lawal Yahaya Gumau Ya Rasu Yana Da Shekara 57
  • Thomas Friedman: Trump Yana Son Ci Gaba Da Zama Shugaban Kasar Amurka Har Abada
  • Tsarin Fansho Na Jihar Jigawa Ya Yi Wa Sauran Jihohi Zarra- Premium Pension
  • MDD Ta CE Sake Tada Komatsar Tattalin Arzikin Kasar Siriya Zau Dauki Shekaru 50 Nan Gaba
  • Ministoci Za Su Fara Gabatar Da Rahoton Ayyuka A Taron Manema Labarai  
  • Gwamna Namadi Ya Kaddamar Da Shirin Da’awah Na Mata A Jihar Jigawa