Masu Kira ta Waya a Shirin FRCN Kaduna Sun Koka Kan Jinkirin Biyan Fansho
Published: 23rd, February 2025 GMT
Masu kira ta waya a shirin Zamani Abokin Tafiya na FRCN Kaduna sun bayyana damuwa kan jinkirin biyan basussukan fansho ga tsofaffin ma’aikata duk da umarnin shugaban ƙasa da aka bayar kwanan nan.
Sun jaddada bukatar jami’an da ke kula da lamarin su hanzarta aiwatar da biyan kuɗaɗen domin girmama sadaukarwar da dattawan ƙasa suka yi da kuma rage cin hanci da rashawa a hidimar jama’a.
Masu kiran sun yi kira ga jami’ai da su nuna kishin ƙasa da tsoron Allah a yayin gudanar da aikinsu domin cika burin al’umma da kuma ci gaban ƙasa.
Alhaji Ibrahim Muhammad Katsina, Isya Soba, Ibrahim Allarama, Umar Aliyu Soba, Shafi’u Nalantawa, da Maza Jiya Soba, waɗanda su ma suka yi kira, sun jaddada bukatar inganta tsaro da rage farashin kayan masarufi bisa ga alkawarin da Gwamnatin Tarayya ta dauka.
SULEIMAN KAURA
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Biyan Fansho Shirye Shirye FRCN
এছাড়াও পড়ুন:
Masu neman yi wa Natasha kiranye ba su cika ƙa’ida ba — INEC
Hukumar zaɓen Nijeriya (INEC), ta bayyana cewa ƙorafin da aka gabatar kan batun yi wa sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti Uduaghan kiranye bai cika ƙa’ida ba.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamishinan bayanai da wayar da kan al’umma na hukumar, Sam Olumekan, ya fitar a yau Talata.
Dalilin da dimokuraɗiyya ta gaza kawo ci gaba a Afirka — Obasanjo Gidauniyar Zakkah ta raba wa marayu 100 kayan sallah a GombeSam Olumekan ya ce waɗanda suka turo ƙorafin kan batun yi wa Sanata Natasha kiranye ba su sanya bayanan da ake buƙata ba kamar yadda Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya na 1999 ya tanada.
Sanarwar ta ce “abin da hukumar ta lura shi ne bayan kawo ƙorafin waɗanda suka jagoranci kawo ƙorafin ba su bayar da adireshi da lambobin waya da kuma adireshin tura saƙon email da za a iya tuntuɓar su ba.
“Adireshin da kawai aka rubuta a jikin takardar shi ne ‘Okene, Jihar Kogi’, wanda wannan bai isa a iya tuntuɓar masu ƙorafin ba,” in ji sanarwar.
Haka nan sanarwar ta ƙara da cewa “lambar wayar jagoran masu turo da koken ne kawai aka saka a wasiƙar, maimakon lambobin wayoyin dukkanin wakilan masu ƙorafin.”
A cikin sanarwar, INEC ta bayyana cewa a shirye ta ke ta bi matakan da kundin tsarin mulki ya shimfiɗa mata na yin irin wannan kiranye da zarar masu ƙorafin sun cika ƙa’idojin da doka ta gindaya.
Sanata Natasha Akpoti na fuskantar kiranye ne tun bayan taƙaddamar da ta ɓarke tsakanin ta da Shugaban Majalisar Dattawan, Sanata Godswill Akpabio, bayan zargin da ta yi masa na yunƙurin cin zarafi na lalata.
Sai dai Majalisar Dattawan ta zargi Natasha da karya dokokin majalisa ta hanyar ƙin komawa sabuwar kujerar da aka sauya mata, da kuma yin hargowa a majalisa, lamarin da ya kai ga dakatar da ita daga majalisar na tsawon wata shida.
Yanzu haka dai INEC ta tabbatar da cewa an kai mata ƙorafin neman yi wa ’yar majalisar kiranye, inda aka tura mata takardu ɗauke da sa hannun rabin masu kaɗa ƙuri’a 474,554 na rumfunan zaɓe 902 da ke mazaɓar ’yar majalisar a ƙananan hukumomin Adavi da Ajaokuta da Ogori/Magongo da Okehi da kuma Okene.