Taron na farko na ministocin harkokin wajen G20 a karkashin shugabancin Afirka ta Kudu ya kasance mai cike da tarihi, domin shi ne taron ministocin wajen kungiyar na farko a nahiyar Afirka, kamar yadda ministan huldar kasa da kasa da hadin gwiwa na Afirka ta Kudu, Ronald Lamola ya bayyana, yayin da yake yabawa da taron, a wani taron manema labarai bayan kammala taron, inda har ila yau ya kara da cewa, taron “mai matukar fa’ida” ya yi gagarumar tattaunawa a kan dabarun da suka shafi yanayin shiyyoyin duniya da tasirinsu a kan gudanar da ayyukansu.

(Abdulrazaq Yahuza Jere)

 

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Mai Pataskum ya buɗe masallacin garin Danga a Yobe

Mai martaba Mai Pataskum, Alhaji Umaru Bubaram Ibn Wuriwa Bauya, ya jagoranci bikin buɗe sabon masallacin Juma’a da aka gina a Garin Danga a Ƙaramar Hukumar Potiskum da ke Jihar Yobe.

Bikin kaddamar da sabon masallacin Juma’ar, wanda ya jawo shugabannin al’umma, malaman addini, da mazauna yankin ya nuna irin gagarumin ci gaba da aka samu a harkokin addinin musulunci a yankin.

Mai Pataskum, wanda ya yi fice wajen bayar da gudunmawa wajen samar da zaman lafiya da ci gaba a yankin, ya yaba da kokarin da masu bayar da tallafi na kasar Malaysia suka yi na gina masallacin, tare da jaddada rawar da yake takawa wajen samar da haɗin kai da ci gaban yankinbmasarautar.

Mai martaba Sarkin ya yi addu’ar fatan alheri ga al’ummar masarautar, jihar Yobe da ma kasa baki ɗaya.

Ya kuma yaba wa yadda kasar ta Malaysia ke taka rawar gani wajen ciyar da addinin musulunci gaba a faɗin duniya.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sin: Manufar Zuba Jarin Amurka Na Matukar Kassara Hadin Gwiwar Kasuwancin Kamfanonin Sin Da Amurka
  • Gwamnatin Katsina Ta Kashe Naira Biliyan 5.7 Wajen Sayen Awaki 40,000 Domin Raba Wa Mata
  • Mai Pataskum ya buɗe masallacin garin Danga a Yobe
  • Iran Ta Bukaci Hanzarta Hukunta Shugabannin ‘Yan Sahayoniyya Kan Laifukan Da Suka Aikata
  • Wang Yi: Sin Za Ta Ci Gaba Da Mara Baya Ga Garambawul Na Kungiyar WTO 
  • Yake-Yaken Kasa Da Kasa Ne Suka Mamaye Taron G20 Na Ministocin Harkokin Wajen Kungiyar A Afirka Ta Kudu
  • Iran Ta Kudiri Anniyar Karfafa Alakarta Da Kasashen Afirka
  • Limamin  Juma’a Na Tehran Ya Jaddada Muhimmancin Hadin Kai A Tsakanin Al’ummar Musulmi
  • Shirin Rigakafin Cututtuka Na UNICEF/GAVI Ya Sami Cikakken Hadin Kan Gwamnatin Jihar Jigawa