Gobara ta ƙone gidaje, amfanin gona da dabbobi a Borno
Published: 23rd, February 2025 GMT
Wata gobara ta tashi a ƙauyen Bukar da ke Ƙaramar Hukumar Konduga a Jihar Borno, ta yi ɓarna mai tarin yawa.
Gobarar ta lalata gidaje, amfanin gona, da dabbobi na miliyoyin Naira, amma babu wanda ya rasa ransa.
’Yan bindiga sun harbe fasto, sun sace wasu a coci Gawuna ne ya lashe zaɓen Gwamnan Kano a 2023 — AtaWani mazaunin ƙauyen ya ce gobarar ta fara ne daga wutar girki a wani gida, sai iska mai ƙarfi ta bazata zuwa wasu gidaje, lamarin da ya sa mutane suka kasa shawo kanta.
Bayan kamawar wutar, sojojin Najeriya da ke yankin sun garzaya domin kai ɗauki.
Sun taimaka wajen kashe wutar tare da ceton tsofaffi da yara.
Kazalika, gobarar ta cinye wani ɓangare na kasuwar ƙauyen, inda ta ƙone shaguna da rumfunan abinci.
Mazauna ƙauyen sun ce yanayin iskar da ake yi a lokacin ya ƙara ta’azzara gobarar, hakan ya sa aka wahala wajen kashe ta.
Duk da hatsarin da ke tattare da wutar, sojoji sun taimaka wajen daƙile gobarar, wanda ya hana ta bazuwa zuwa wasu wurare, ciki har da makarantar ƙauyen.
Shugabannin yankin sun nuna godiyarsu ga sojojin da suka kawo musu ɗauki cikin gaggawa.
“Ba don taimakon Allah da na sojoji ba, gobarar na iya haddasa asarar rayuka,” in ji wani mazaunin ƙauyen, Bukar Usman.
A halin yanzu, Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Borno (SEMA), ta tura tawaga domin tantance asaea tare da raba kayan agaji ga waɗanda gobarar ta shafa.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Ɗan sa-kai ya kashe matasa biyu a Borno
An kama wani jami’in rundunar sa-kai ta JTF, Modu Mallam Gana mai shekaru 27 a garin Monguno, bisa zarginsa da harbin wasu gungun matasa wanda ya yi sanadin mutuwar mutane biyu tare da raunata daya.
Wata majiyar leƙen asiri ta shaida wa Zagazola Makama cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 6:15 na safiyar ranar 21 ga Maris, 2025, a lokacin da wasu matasa suka tsaya a gaban ofishin dakarun da ke Unguwar Bakin Kasuwa, a Karamar Hukumar Monguno.
Mahaifiyar Gwamnan Katsina ta rasu Yadda ake noman gurjiyaMajiyar ta ce wanda ake zargin Modu Mallam Gana ya harzuka da tsayarwar matasan a bakin ofishinsu, lamarin da ya bude musu wuta.
Wadanda abin ya shafa — Ya’zainab Bum da Goni Mohammed Ahmadu — sun mutu nan take yayin da Hamsatu Ali ta samu munanan raunuka kuma aka kwantar da ita a babban asibitin Monguno.
Sai dai an tabbatar da mutuwar Ya’zainab Bum da Goni Mohammed Ahmadu, inda aka mika wa iyalansu gawarwakinsu domin yi musu jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada yayin da Hamsatu Ali tana kwance a asibiti tana jinya.
Majiyar ta ce an kama wanda ake zargin nan take, kuma aka mika shi ga ‘yan sanda don gudanar da binciken da ya dace da shi.