Aminiya:
2025-02-23@19:04:21 GMT

Fasinjoji 4 sun rasu yayin da bas ta kama da wuta a Jigawa

Published: 23rd, February 2025 GMT

Mutane huɗu sun rasa rayukansu, wasu 10 kuma sun samu raunuka bayan wata motar bas ƙirar Hummer ta kama da wuta a garin Gwaram da ke Jihar Jigawa.

Lamarin ya faru da misalin ƙarfe 4 na yammacin ranar Asabar, a kusa da makarantar sakandaren gwamnati ta Government Girls Unity Secondary School da ke Gwaram.

Gobara ta ƙone gidaje, amfanin gona da dabbobi a Borno  Za a kafa ƙarin makarantu a Zariya — Abbas Tajudeen

Kakakin ’yan sandan Jihar Jigawa, SP Lawan Adam, ya tabbatar da faruwar hatsarin cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi.

Ya ce motar ta taso daga Ƙaramar Hukumar Zaki daga Jihar Bauchi zuwa ƙauyen Ribadi da ke Ƙaramar Hukumar Gwaram.

Sanarwar ta bayyana cewa motar na ɗauke da fasinjoji 44, wanda suka haɗa da manya 25 da yara 19.

Kakakin, ya ce wutar ta samo asali ne daga katifa da aka ɗaure a bayan motar, kusa da bututun fetur.

Mutum 10 da suka samu raunuka an garzaya da su asibitin Gwaram, yayin da aka ceto sauran fasinjojin ba tare da sun ji ciwo ba.

Waɗanda suka rasu sun haɗa da Zuwairah Hassan mai shekaru 40, Fatima Hassan mai shekaru biyar.

Sauran sun haɗa da Iyatale Hassan mai shekaru uku da Halima Muhammad mai shekaru 10, dukkaninsu ‘yan ƙauyen Saldiga da ke Ƙaramar Hukumar Zaki, a Jihar Bauchi.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Yan Sanda Hatsari Jigawa rasuwa mai shekaru

এছাড়াও পড়ুন:

’Yan sanda sun daƙile satar mutane, sun kama wasu 3 a Borno

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Borno, ta daƙile wani yunƙuri da ’yan bindiga suka yi na sace wani mutum a Sabon Garin Lassa da ke Ƙaramar Hukumar Askira Uba.

Rundunar ta kuma cafke wasu mutum uku tare da ƙwato wata bindiga ƙirar gida a hannunsu.

Babban mai kai wa Bello Turji makamai ya shiga hannu NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Ba Za Mu Sauke Farashin Burodi Ba —’Yan kasuwa

Majiyoyin tsaro sun shaida wa Zagazola Makama cewa, lamarin ya faru ne a ranar 20 ga watan Fabrairu da misalin karfe 1 na dare.

Wasu ’yan bindiga huɗu suka kai hari gidan Mohammed Abubakar, mazaunin Sabon Gari Lassa, da nufin sace shi.

“Wanda suka yi niyyar sacewa ya yi ƙoƙarin kare kansa da adda, lamarin da ya tilasta wa maharan tserewa ba tare da sun cimma burinsu ba”, in ji majiyar.

Bayan haka, Abubakar, ya gaggauta kiran ’yan sanda, inda tare da haɗin gwiwar ’yan banga, jami’an tsaro suka bi sahun ’yan bindigar zuwa maɓoyarsu.

A sakamakon haka, rundunar ‘yan sanda ta cafke mutum uku da ake zargi, dukkaninsu mazauna ƙauyen Gajali da ke Ƙaramar Hukumar Askira Uba.

“Haka kuma an ƙwato wata bindiga da aka ƙera a gida daga hannun waɗanda ake zargin,” in ji majiyar.

Rundunar ’yan sandan jihar, ta yaba da yadda jami’an tsaro suka mayar da martani cikin gaggawa, tare da yin kira ga al’umma da su kasance masu lura da duk wani abu da ba su saba gani ba.

Ta kuma buƙaci su gaggauta kai rahoto ga jami’an tsaro domin ɗaukar mataki a kan lokaci.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sharki: Takaitaccen Rayuwar Sayyid Shahid Hassan Nasarallah (r)
  • Sibil Difens ta cafke mutum 17 kan aikata sata a Yobe
  • Da Ɗumi-ɗumi: Sanata Lawal Yahaya Gumau Ya Rasu Yana Da Shekara 57
  • Tsarin Fansho Na Jihar Jigawa Ya Yi Wa Sauran Jihohi Zarra- Premium Pension
  • ’Yan sanda sun daƙile satar mutane, sun kama wasu 3 a Borno
  • UNICEF Ya Jinjinawa Jihar Jigawa
  • Shirin Rigakafin Cututtuka Na UNICEF/GAVI Ya Sami Cikakken Hadin Kan Gwamnatin Jihar Jigawa
  • Gwamna Namadi Ya Kaddamar Da Shirin Da’awah Na Mata A Jihar Jigawa
  • Ɗaliba ta rasu yayin da gini ya rufta a GGTC Potiskum