Cittar Da Ake Fitarwa kasashen Waje Ta Ragu Da Kashi 74 Cikin 100
Published: 23rd, February 2025 GMT
dimbin Asarar Da Manoman Cittta Suka Tabka:
Shugabar kungiyar manoman Citta da sarrafata ta kasa (GGPMAN) Florence Edwards, ta alakanta samun raguwar Cittar da ake fitarwa daga kasar nan zuwa kasashen ketare da barkewar cutar da ta lalata gonakin wasu manomanta.
Florence ta kara da cewa, akasarin irin samfurin Cittar da manoman ke shukawa a fadin kasar nan, sun shafe sama da shekaru 20 suna amfani da shi.
Ita ma wata manomiyar Cittar a Jihar Kaduna, Joy Bolus ta bayyana cewa, ta kashe sama da Naira miliyan daya a shekarar da ta gabata wajen aikin noman Cittar a tata gonar, ta hanyar yin hadaka da miinta, amma saboda barkewar cutar a bara, hakan ya jawo gonar ta lalace baki-daya.
“A kakar noman bara, ni da mijina mun yi asarar sama da Naira 800, 000, bayan barkewar cutar”, a cewar Joy.
Duk kokarin da gwamnatin tarayya ta yi na magance yaduwar cutar, hakan bai samar da wani sakamako na a zo a gani ba, musamman ganin yadda manomanta a Jihohin Kaduna, Kano da wasu yankuna biyu na kasar da aka fi yin noman ke ci gaba da kirgar irn asarar da suka tabka sakamakon barkewar cutar.
karamin Ministan Ma’aikatar Aikin Noma da Samar da Wadataccen Abinci, Sabi Abdullahi ya bayyana cewa, tun bayan barkewar cutar a 2023, manoman da annobar cutar ta afkawa a gonakinsu, sun yi asarar kimanin Naira biliyan 12.
A watan Oktoban 2023, gwamnatin tarayya; ta samar wa da manoman, musamman na jihohin da aka fi yin nomanta tallafin Naira biliyan 1.6 tare kuma da raba musu magungunan feshin cutar, domin rage musu radadin annobar.
Jaridar BusinessDay, tun da farko ta ruwaito cewa, farashin Cittar ya karu da rubi shida a shekaru biyu da suka gabata, inda kowane buhunta daya a 2023 ya kai Naira 50, 000, sannan kuma ya karu zuwa Naira 300,000 a shekarar 2025.
Wasu manoman, sun alakanta hauhawar farashin da barkewar cutar a 2023, inda hakan ya jawo wa manoman nata yin asarar kimanin Naira biliyan 12.
A cikin kasafin kudi na 2025, an kara wa Hukumar Samar da Ingantaccen Irin Noma ta kasa (NASC) kashi 36, kimanin Naira biliyan 3.8, sabanin Naira biliyan 2.8 da aka ware mata a kasafin kudi na 2024, amma abin takaici; har yanzu manoman kasar, ba su iya samun ingantaccen Irin ba.
A cewar Hukumar Samar Wadattacen Abinci da Bunkasa Aikin Noma (FAO) ta duniya ta ce, a fidin duniya kaf; Nijeriya na daya daga cikin kasashen da ke kan gaba wajen noman Citta, duba da yadda kasar ta noma kimanin tan 781,000 a 2023.
Mafi akasari, Nijeriya na fitar da Cittar da aka noma a kasar ne zuwa kasuwannin Gabas ta Tsakiya ko kuma Nahiyar Turai.
“Manoman Citttar, na bukatar samar musu da Irinta, mai bijer wa kowace irin cutar da ke yi wa gonakinsu illa tare kuma da yin gwajin kasar da ake noma ta, don gano inda cutar ke fara kunno kai”, in ji Florence.
এছাড়াও পড়ুন: