A jiya Asabar 22 ga wannan wata, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya yi bayani ga kafofin watsa labaru na kasar Sin bayan da ya kammala ziyararsa a Birtaniya da Ireland, da halartar taron kiyaye tsaro na Munich karo na 61, da shugabantar taron kolin kwamitin sulhun MDD a birnin New York, da kuma halartar taron ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar G20 a kasar Afirka ta Kudu.

A matsayin kasar da take shugabantar kwamitin sulhun MDD a wannan wata, kasar Sin ta yi kira ga taron koli na kwamitin mai taken “Bin ra’ayin bangarori daban daban da yin kwaskwarima kan kyautata aiwatar da harkokin duniya”. Inda game da hakan, Wang Yi ya bayyana cewa, kasar Sin ta yi bayani game da ra’ayinta na kafa tsarin daidaita harkokin duniya cikin adalci, wato tabbatar da zaman daidaito kan ikon mallakar kasa, da tabbatar da adalci da yin hadin gwiwa da kuma bin taswirar aiwatar da ayyuka, kuma ra’ayin na kasar Sin ya samu amincewar kasashen da suka halarci taron.

Game da kara kaimin samar da yanayin dogaro da bangarori masu yawa maimakon daya tilo, Wang Yi ya yi nuni da cewa, yin hakan a duniya shi ne muhimmin ra’ayi da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar, kuma shi ne kyakkyawan fatan da kasar Sin ta nuna wa duniya. Kana, kasar Sin za ta tabbatar da tsarin dogaro da bangarori masu yawa, da samar da gudummawa ga duniya yayin da ake fuskantar sauyin duniya.

Ban da wannan kuma, Wang Yi ya bayyana cewa, za a gudanar da taron kolin shugabannin kasashen kungiyar G20 a watan Nuwamban bana a nahiyar Afirka a karo na farko. Wannan shi ne lokacin da nahiyar Afirka ta samu cikakkiyar dama a kungiyar G20 da kuma aiwatar da harkokin duniya, wanda ya shaida cewa, shi ne babban canji a tarihi ga yanayin tattalin arziki da siyasa na duniya, kuma lamarin yana da babbar ma’ana. A gun taron ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar G20 a wannan karon a birnin Johannesburg dake Afirka ta Kudu kuwa, kasar Sin ta ce ya kamata a kara sauraron ra’ayin kasashen Afirka, da maida hankali ga batutuwan Afirka, da nuna goyon baya ga Afirka, da rike damar hadin gwiwa ta kungiyar G20 don sa kaimi ga samun ci gaba da wadata a nahiyar ta Afirka. Wannan ra’ayi ya samu amincewar kasa da kasa. (Zainab Zhang)

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: kasar Sin ta kungiyar G20

এছাড়াও পড়ুন:

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Taimakawa Shirye-shiryen Zabe A Jamhuriyar Afrika Ta Tsakiya

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Taimakawa Shirye-shiryen Zabe A Jamhuriyar Afrika Ta Tsakiya

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ministan Wajen Sin Ya Yi Kiran Hadin Gwiwar Kasashen G20 Don Gina Duniya Mai Adalci Da Ci Gaba Na Bai-daya
  • Bayan Kalubalantar Ra’ayin Amurka Kan Gaza Trump Ya Ce Furucinsa Shawara Ce Kawai
  • Wang Yi: Sin Za Ta Ci Gaba Da Mara Baya Ga Garambawul Na Kungiyar WTO 
  • Yake-Yaken Kasa Da Kasa Ne Suka Mamaye Taron G20 Na Ministocin Harkokin Wajen Kungiyar A Afirka Ta Kudu
  • Iran Ta Kudiri Anniyar Karfafa Alakarta Da Kasashen Afirka
  • DRC : Kwamitin Tsaro Na MDD, Ya Yi Da Goyan Bayan Da Rwanda Ke Bai Wa ‘Yan Tawayen M23
  • Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Taimakawa Shirye-shiryen Zabe A Jamhuriyar Afrika Ta Tsakiya
  • Kasar Sin Ta Bukaci G20 Ta Zama Karfin Tabbatar Da Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankali A Duniya
  • Jami’an Diblomasiyya Daga Kungiyar G20 Da Dama Sun Isa Afrika Ta Kudu