Aminiya:
2025-03-26@06:40:31 GMT

Arewa na buƙatar haɗa kai da Kudu Maso Kudu don ceto Najeriya — El-Rufai

Published: 23rd, February 2025 GMT

Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya buƙaci manyan ‘yan siyasa daga yankin Arewa da Kudu Maso Kudu su haɗa kai gabanin zaɓen 2027.

El-Rufai, ya yi wannan kira ne yayin da ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan marigayi dattijo kuma jagoran yankin Neja Delta, Edwin Clark.

Babu ɗan Arewa mai hankali da zai yi tallan APC a 2027 – Jigo a PDP Fasinjoji 4 sun rasu yayin da bas ta kama da wuta a Jigawa

A cewarsa, Najeriya tana cikin matsala mai tsanani kuma tana buƙatar ɗauki cikin gaggawa.

“A shekarun baya, Arewa da Kudu Maso Kudu sun kasance abokan siyasa,” in ji El-Rufai.

“Kada mu manta da hakan. Mu koma kam wannan haɗin kai. Mu ceci wannan ƙasa domin tana buƙatar ceton gaggawa. Dole ne mu ɗauki matakin ceton ƙasar nan.”

Maganganunsa sun zo ne yayin da ake raɗe-raɗin cewa yana shirin sauya sheƙa daga jam’iyyar APC.

A makonnin da suka gabata, ya gana da ’yan siyasa daga jam’iyyun adawa bayan wani saɓani tsakaninsa da jam’iyyar APC mai mulki da kuma gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

El-Rufai, wanda ya je ziyarar ta’aziyyar tare da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya yaba da rawar da Atiku ya taka wajen kawo sauye-sauyen tattalin arziƙi a lokacin mulkin Shugaba Olusegun Obasanjo.

Segun Showunmi, tsohon mai magana da yawun yaƙin neman zaɓen Atiku, ya tabbatar da cewa wannan ganawar tana cikin shirye-shiryen siyasa gabanin zaɓen 2027.

A watan Janairu, El-Rufai ya gana da Hamza Al-Mustapha, tsohon hadimin marigayi Janar Sani Abacha, da Shehu Gabam, shugaban jam’iyyar SDP, da wasu ’yan siyasa a Abuja.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Arewa Edwin Clark Haɗin Kai rasuwa Siyasa ta aziyya

এছাড়াও পড়ুন:

NIDCOM: An Ceto ‘Yan Nijeriya Sama Da 950 Daga Gidajen Kurkuku A Libya

Hukumar kula da ‘yan Nijeriya mazauna ƙasashen ƙetare (NIDCOM), ta bayyana cewa an kuɓutar da ‘yan Nijeriya 956 daga gidajen yarin Libya tare da mayar da su gida cikin watanni ukun farkon shekarar 2025.

Shugabar hukumar, Hon. Abike Dabiri-Erewa, ta ce waɗanda aka dawo da su sun haɗa da mata 683, maza 132, yara 87, da jarirai 54.

An samu nasarar mayar da su ne sakamakon haɗin gwiwa tsakanin NIDCOM, Hukumar ‘Yan Gudun Hijira ta Duniya (IOM) da kuma Hukumar Kula da Baƙin Haure da waɗanda rikici ya raba da matsugunansu (NCRMI).

A cewar sanarwar da NIDCOM ta fitar, an dawo da su ne kashi-kashi daga watan Janairu zuwa Maris 2025.

A ranar 28 ga Janairu, an dawo da mutum 152. A ranakun 11, 19, da 25 ga Fabrairu, an dawo da mutum 484. A ranakun 4 da 18 ga Maris, an dawo da mutum 320.

Dabiri-Erewa ta ƙara da kira ga ‘yan Nijeriya da su guji tafiya ƙetare ta ɓarauniyar hanya, musamman ta Libya, wacce ke fama da matsaloli da rikici.

Ta kuma jaddada cewa wajibi ne ‘yan Nijeriya su bi hanyoyin da doka ta tanada idan suna son yin hijira, domin guje wa hatsarin da ke tattare da tafiya ta haramtacciyar hanya.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • NIDCOM: An Ceto ‘Yan Nijeriya Sama Da 950 Daga Gidajen Kurkuku A Libya
  • Dalilin da dimokuraɗiyya ta gaza kawo ci gaba a Afirka — Obasanjo
  • Gwamnatin Tarayyar Najeriya Ta Kafa Rundunar Daukin Gaggawa Don Magance Matsalolin Tsaro
  • SDP: Ba Mu Yi Wa Kowa Alƙawarin Takarar Shugaban Ƙasa Ba
  • NAJERIYA A YAU: Yadda Ake Yi Wa ‘Yan Majalisar Ƙasa Kiranye
  • An yi wa Jakadan Afirka ta Kudu da Amurka ta kora tarbar Jamurumai bayan komawarsa gida
  • Sule Lamido Ya Soki Rabon Abinci da Seyi Tinubu Ya Yi A Arewa
  • NAJERIYA A YAU: Yadda watan Ramadana ke tasiri a harkokin kasuwanci
  • Gwamnonin Arewa sun yi wa Radda ta’aziyyar rasuwar mahaifiyarsa
  • Yadda Tinubu Ya Shirya Wa Kansa Mafitar Siyasa Kafin Zaben 2027