Birtaniya Da Faransa suna Son Aikewa Da Sojojin Turai 30,000 Kasar Ukiraniya
Published: 23rd, February 2025 GMT
Jaridar Wall Satreet Journal ta ambaci cewa kasashen Faransa da Birtaniya suna shirya yiyuwar aikewa da sojojin tabbatar da zaman lafiya a cikin kasar Ukiraniya idan an tsagaita wutar yaki.
Jaridar ta Amurka ta kuma kara da cewa; Idan an kai ga cimma tsagaita wutar yaki to da akwai yiyuwar turawan za su aike da sojojin zaman lafiya da za su kai 30,000 daga cikin har da na kasar Switzerland.
Sai dai kuma aiwatar da shirin na turai yana da alaka ne da yadda Donald Trump zai amince da kasarsa ta taka rawa, idan har Rasha ta kai wa turawan hari, ko ta keta yarjejeniyar tsagaita wuta, kamar yadda jaridar ta ambato wani jami’in turai din yana fada.
Jaridar ta kara da cewa turawan ba za su bukaci Amukan ta aike da sojoji tare da su zuwa Ukiraniya din ba, sai dai za su bukaci taimakonta da kayan aikin da ba su da su.
A ranar Alhamis mai zuwa ne ake sa ran cewa Fira ministan Birtaniya Sir Keir Rodney Starmer zai tattauna shirin nasu na turai da shugaban kasar Amurka Donald Trump.
A gefe daya, kwamandan sojojin kasar Switzerland Laftanar Janar Thomas Sussli ya bayyana cewa, kasarsa za ta iya taimakawa da wani adadi na sojojin zaman lafiya anan gaba,idan har gwamnatin Ukiraniyan ta bukaci hakan.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Aljeriya ta yi barazanar korar jami’an diflomasiyyar Faransa 12
Rikicin diflomasiyya tsakanin Paris da Algiers na dada kamari, inda Aljeriya ta bukaci wasu jami’an diflomasiyyar Faransa 12 da su fice daga kasar cikin sa’o’i 48.
Ministan harkokin wajen Faransa Jean-Noël Barrot ya sanar cewa, Aljeriya ta bukaci jami’an diflomasiyyar Faransa da su fice daga kasar bayan kama wasu ‘yan kasar Aljeriya uku a Faransa.
“Ina kira ga hukumomin Aljeriya da su yi watsi da wannan matakin, inda ya kara da cewa: “Idan har aka ci gaba da yanke shawarar korar wakilanmu, ba mu da wani zabi illa mu mayar da martani cikin gaggawa.”
Shekaru da dama, alakar diflomatoyyar da ke tsakanin Aljeriya da Faransa ta yi tsami.
A farkon watan Afrilu, ministan harkokin wajen Faransa ya je kasar Aljeriya, domin kokarin warware matsalolin da suka jefa kasashen biyu cikin tabarbarewar diflomasiyya.
Bayan ganawa da shugaban kasar Aljeriya, Abdelmadjid Tebboune, Jean-Noël Barrot ya bayyana muradin kasashen biyu na “sake gina dangantakar abokantaka.”
A daidai lokacin da ake fuskantar tsamin dangantaka tsakanin Algiers da Paris, ofishin mai gabatar da kara na Faransa ya tuhumi, wasu ‘yan kasar Aljeriya uku, a ranar 11 ga Afrilu, ciki har da wani jami’in ofishin jakadanci, da zarginsu da hannu a sace wani dan adawar gwamnatin Algeria, Amir Boukhors, da aka sani da “AmirDZ na Paris” a cikin 2024.
Aljeriya ta yi kakkausar suka a ranar Asabar, 12 ga Afrilu, don nuna adawa da kamawa da tsare daya daga cikin jami’an ofishin jakadancinta a kasar Faransa tare da neman a gaggauta sakin shi.