Kasar Sin Ta Zayyana Muhimman Ayyukanta Na Zurfafa Gyare-gyare A Yankunan Karkara Da Inganta Raya Su.

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Birtaniya Da Faransa suna Son  Aikewa Da Sojojin Turai 30,000 Kasar Ukiraniya

Jaridar Wall Satreet Journal ta ambaci cewa kasashen Faransa da Birtaniya suna shirya yiyuwar aikewa da sojojin tabbatar da zaman lafiya a cikin kasar Ukiraniya idan an tsagaita wutar yaki.

Jaridar ta Amurka ta kuma kara da cewa; Idan an kai ga cimma tsagaita wutar yaki to da akwai yiyuwar turawan za su aike da sojojin zaman lafiya da za su kai 30,000 daga cikin har da na kasar Switzerland.

Sai dai kuma aiwatar da shirin na turai yana da alaka ne da yadda Donald Trump zai amince da kasarsa ta taka rawa, idan har Rasha ta kai wa turawan hari, ko ta keta yarjejeniyar tsagaita wuta, kamar yadda jaridar ta ambato wani jami’in turai din yana fada.

Jaridar ta kara da cewa turawan ba za su bukaci Amukan ta aike da sojoji tare da su zuwa Ukiraniya din ba, sai dai za su bukaci taimakonta da kayan aikin da ba su da su.

A ranar Alhamis mai zuwa ne ake sa ran cewa Fira ministan Birtaniya Sir Keir Rodney Starmer zai tattauna shirin nasu na turai da shugaban kasar Amurka Donald Trump.

A gefe daya, kwamandan sojojin kasar Switzerland  Laftanar Janar Thomas Sussli ya bayyana cewa, kasarsa za ta iya taimakawa da wani adadi na sojojin zaman lafiya anan gaba,idan har gwamnatin Ukiraniyan ta bukaci hakan.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ruguntsumin Balaguron Bikin Bazara Na Bana A Tsakanin Manyan Yankunan Sin Ya Kafa Tarihi  
  • Kakakin Ma’aikatar Tsaron Kasar Sin Ya Yi Fatali Da Zargin Australia A Kan Atisayen Sojojin Kasar
  • Birtaniya Da Faransa suna Son  Aikewa Da Sojojin Turai 30,000 Kasar Ukiraniya
  • ‘Yan Bindiga Sun Kashe Wani Mutum Tare Da Sace Mutum Biyu A Kaduna
  • Kungiyar Hizbullah Ta Lebanon Ta Jaddada Rashin Amincewarta Da Mika Kan Kasar Ga Amurka Da Haramtacciyar Kasar Isra’ila
  • Thomas Friedman: Trump Yana Son Ci Gaba Da Zama Shugaban Kasar Amurka Har Abada
  • Gwamnatin Filato ta dakatar da haƙar ma’adinai saboda matsalar tsaro
  • MDD Ta CE Sake Tada Komatsar Tattalin Arzikin Kasar Siriya Zau Dauki Shekaru 50 Nan Gaba
  • Trump Yana Son Ganin Bayan Shugaban Kasar Ukraine Volodimir Zelezky Daga Kujerar Shugabancin Kasarsa