Matakin Amurka Na Takaita Zuba Jari Zai Cutar Da Wasu Da Ita Karan Kanta.

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

’Yan bindiga sun harbe fasto, sun sace wasu a coci

’Yan bindiga sun kai hari wata coci da ke yankin Ogwashi-Uku a Jihar Delta, inda suka yi awon gaba da masu ibada a daren ranar Juma’a.

Sun harbi fasto sannan suka sace masu i ada shida a cocin, lamarin da ya jefa al’umma cikin firgici.

Gawuna ne ya lashe zaɓen Gwamnan Kano a 2023 — Ata Jami’ar Sojoji ta BIU ta ƙaddamar da taron magance zamba

Sun kai harin ne da misalin ƙarfe 10 na dare kusa da Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Delta.

Maharan sun harbi fasto, Apostle Divine Omodia, wanda yanzu haka yake kwance a asibiti.

Mutanen yankin suna cikin fargaba kan rashin tsaro a wuraren ibada, inda suke roƙon gwamnati ta ceto mutanen da aka sace tare da kama waɗanda suka kai harin.

Matar faston, Fasto Faith Omodia, ta bayyana jimaminta kan faruwar lamarin.

Ta ce ’yan bindigar sun buɗe wuta a cikin cocin.

“Na kwanta da jaririna a cikin coci sai na ji harbe-harbe. Kafin na ankara, harsasai sun fara shigowa cikin ɗakin da muke ciki.

“Ɗaya daga cikinsu ya harbe ni, amma harsashin bai shiga jikina ba. Sai dai kawai na ga wuta,” in ji ta.

Ta kuma ce an harbi mijinta a ƙafarsa, sannan ya rasa yatsu biyu.

Bayan haka, ’yan bindigar sun tattara masu ibada, tare da yin awon gaba da mutum shida, ciki har da masu gadin cocin biyu.

Mutanen da aka sace sun haɗa da Helen Onwuamaeze, Ariyo Emmanuel, Chike Okolo, da Blessing Waye, tare da masu gadi biyu da ba a bayyana sunayensu ba.

Rundunar ’yan sandan Jihar Delta ba ta tabbatar da faruwar harin ba tukuna.

Lokacin da aka tambayi kakakin rundunar, Bright Edafe, ya ce babu wani rahoto da aka kai ofishin ’yan sanda kan harin.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  •  Sheikh Zakzaky:  Gwagwarmayar Musulunci A Lebanon Ta Sake Jaddada Kanta
  • Sin: Manufar Zuba Jarin Amurka Na Matukar Kassara Hadin Gwiwar Kasuwancin Kamfanonin Sin Da Amurka
  • Cittar Da Ake Fitarwa kasashen Waje Ta Ragu Da Kashi 74 Cikin 100
  • ’Yan bindiga sun harbe fasto, sun sace wasu a coci
  • Tawagar Iran A Majalisar Dinkin Duniya Ta Kare Matakin Sayar Da Jirgin Samanta Mara Mataki Ciki
  • Sanata Katung ya bayyana damuwa kan ƙaruwar ta’addanci a kudancin Kaduna
  • Sanata Katung ya damu kan yadda wasu ke ta’azzara ta’addanci a kudancin Kaduna
  • Sanata Katung ya damu kan yadda wasu ta’azzara ta’addanci a kudancin Kaduna
  • Najeriya ta taɓarɓare bayan mulkin IBB – Obi