Adadin balaguron fasinjoji a tsakanin manyan yankuna na fadin kasar Sin yayin ruguntsumin bikin Bazara na all’ummar Sinawa na tsawon kwanaki 40, wanda aka fi sani da Chunyun, ya kai biliyan 9.02, kamar yadda bayanan hukuma suka nunar a yau Lahadi.

A cewar tawagar da aka nada ta musamman domin tabbatar da nasarar balaguron al’umma ba tare da wata matsala ba lokacin Chunyu da aka kammala jiya Asabar, alkaluman bana sun nuna an samu karuwar kashi 7.

1 cikin dari a kan adadin da aka samu na daidai irin wannan lokacin a shekarar 2024. (Abdulrazaq Yahuza Jere)

 

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Wasu manyan ’yan Nijeriya sun yi wa Gwamna Radda ta’aziyya a Saudiyya

Wasu manyan ’yan Nijeriya da suka tafi Umarah sun yi wa Gwamnan Katsina Dikko Umar Radda ta’aziyya a Saudiyya.

A safiyar Lahadi ce dai Allah Ya karɓi rayuwar mahaifiyar Gwamnan, Hajiya Safara’u Umaru Baribari bayan shafe tsawon lokaci tana jinya a Jihar Katsina.

Wata mata ta haifi jaririn da ba nata ba NAJERIYA A YAU: Yadda watan Ramadana ke tasiri a harkokin kasuwanci

Bayan rasuwar ce gwamnoni da wasu fitattun ’yan siyasa da a halin yanzu suna ƙasa mai tsarki suka kai wa Gwamna Radda ziyara domin jajanta masa dangane da wannan babban rashi.

Daga cikin gwamnonin akwai Mohammed Umar Bago na Jihar Neja, da Farfesa Babagana Zulum na Jihar Borno da Gwamna Uba Sani na Kaduna, da Dauda Lawal Dare na Zamfara da kuma Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Arewa, Gwamna Inuwa Yahaya na Jihar Gombe

Sauran fitattun ’yan siyasar da suka ziyarci Gwamna Radda sun haɗa da Shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje da tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, da tsohon Gwamnan Bauchi, Ahmed Mu’azu.

Akwai kuma fitaccen attajirin nan kuma ɗan kasuwa, Alhaji Dahiru Mangal da kuma tauraron tawagar ƙwallon ƙafar Nijeriya ta Super Eagles, Ahmed Musa da su ma suka jajanta wa gwamnan a kan rashin.

Dukkansu sun bayyana alhini tare da roƙon Allah Ya jiƙan Hajiya Safara’u Ya sa ta huta.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sudan: RSF ta hana kayan agaji a yankunan da ke a karkashin ikonta
  • Kasuwar Kayayyakin Masarufi Ta Sin Za Ta Ci Gaba Da Nuna Yanayin Bunkasa Bisa Daidaito A Bana
  • ‘Yan ta’adda Sun Kai Hari Sansanin Sojoji, Sun Kashe Uku A Borno
  • Gwamnatin Tarayyar Najeriya Ta Kafa Rundunar Daukin Gaggawa Don Magance Matsalolin Tsaro
  • Kantoman Ribas ya naɗa sabon Sakataren Gwamnati
  • ECOWAS Za Ta Yi Bikin Cika Shekaru 50 Da Kafuwa
  • Yawan Ziyarar Da ‘Yan Siyasa Da ‘Yan Kasuwar Amurka Ke Kawowa Sin Ya Zo Da Mamaki
  • Wasu manyan ’yan Nijeriya sun yi wa Gwamna Radda ta’aziyya a Saudiyya
  • Fiye Da Dalibai 4,200 Suka Amfana Da Tallafin Ilimi Na Sanata Solomon Adeola
  • Ko Raunin ‘Yan Wasa Zai Rage Wa Barcelona Karsashi A Kakar Bana?