Aminiya:
2025-02-24@09:26:09 GMT

Ana zargin malami da azabtar da ɗalibi saboda shan mangwaro a makaranta

Published: 24th, February 2025 GMT

Ana zargin malamin makarantar Aliyu Mustapha Academy da ke Jimeta a Jihar Adamawa kan wuce gona da iri da kuma azabtar da wani ɗalibinsa a dalilin shan mangwaro a lokacin ‘break’ a harabar makarantar.

Aminiya ta ruwaito cewa a lokacin da ake tsaka da hutun tara ne malamin yan kama ɗalibin yana shan mangwaro, inda ya lakaɗa wa ɗalibin dukan tsiya.

Shaidu sun ce har da naushi malamin ya riƙa yi wa ɗalibin, lamarin da ya sa taron ya ƙuƙƙuje tare da barin sa da tabbai a jikinsa.

Malamin yana tsaka da dukan ɗalibin ne mahaifin yaron ya je makarantar domin tabbatar da biyan kudin makarantar ɗan nasa.

NAJERIYA A YAU: Matakan Kariya Daga Cutar Ƙyandar Biri Har yanzu Najeriya na buƙatar shugabanni nagari – Sheikh Gumi

Ganin halin da ya iske ɗan nasa a sai ya sanya baki, amma malamin bai dakata ba da naushin yaron.

Mahaifin mai suna Bashiru Haman, ya ce, “Na kaɗu da ganin ana dukan yaron haka, na yi ƙoƙarin in ƙwace shi amma malamin ya ƙi barin sa. Daga nan sai an kai ƙara wajen shugabar makarantar, Misis Amanda Pam, Amma sai ta umarce ni da in fice daga harabar makarantar.”

Babbar Sakatariyar Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Adamawa, A’isha Yanar ta tabbatar da faruwar lamarin. Ta ce, “ma’aikatar ta samu wasikar ƙorafin mahaifin ɗalibin kuma ta fara gudanar da bincike domin daukar matakin da ya dace. Za kuma mu ɗauki matakan da suka kamata domin hana faruwar irin haka a nan gaba.”

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Adamawa ta ce ta fara gudanar da bincike kan lamarin, kamar yadda kakakinta, Dankombo Morris, ya sanar.

Ya ce, “muna kira da duk masu wani bayani game da abinda ya faru da su taimaka mana da bayanai a wannan bincike da muke gudanarwa.”

A halin yanzu dai yaron mai suna Jaafar yana fama da jinya a yayin da iyayensa suke neman a ƙwato masa haƙƙi kan azabtarwar da aka yi masa.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Ɗalibi Jihar Adamawa Shan mangwaro

এছাড়াও পড়ুন:

Wani mutum ya yi wa agolarsa fyaɗe ta samu juna biyu

Rundunar ’yan sandan Jihar Legas ta cafke wani mutum mai shekaru 28, Samuel Alfred bisa zargin yi wa wata agolarsa fyaɗe har ta samu juna biyu.

An cafke mutumin ne tare da wani abokinsa, Ikechukwu Obi mai shekaru 30 kan zargin wannan aika-aikar.

An haifi alade mai fuskar mutum a Philippines Ko Real Madrid za ta iya lashe Gasar Zakarun Turai bana?

Bayanai sun ce ababen zargin sun kai budurwar mai shekaru 14 wani ɗaki da ke yankin Ojo na jihar ta Legas inda suka raba ta da budurcinta.

Mai magana da yawun rundunar, Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da faruwar lamarin wanda ya ce mahaifiyar yarinyar mai suna Deborah ce ta kai ƙorafi ofishinsu da ke Okokomaiko.

Hundeyin ya ce za a gurfanar da ababen zargin biyu a gaban kuliya domin su girbi abin da suka shuka.

“A halin yanzu yarinyar tana ɗauke da ciki da har ya kai watanni tara kuma za a miƙa lamarin zuwa kotu,” in ji Hundeyin.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Yadda jama’a suka kama ɗan shekara 65 ɗauke da bindiga
  • Jami’ar Sojoji ta BIU ta ƙaddamar da taron magance zamba
  • An kama mutum biyu kan kisan wata mata saboda maita
  • Shan Maganin Fitar Da Zaƙi Kafin Haihuwa
  • Wani mutum ya yi wa agolarsa fyaɗe ta samu juna biyu
  • Haɗarin mota ya laƙume rayuka 12 a Neja
  • Saudiyya Za Ta Haramta Shan Giya Lokacin Gasar Kofin Duniya
  • Thomas Friedman: Trump Yana Son Ci Gaba Da Zama Shugaban Kasar Amurka Har Abada
  • Tashar Jiragen Sama Ta Rafikul Hariri Int. Na Birnin Beirut Yana Ciki Da Masu Shiga Kasar Saboda Jana’izar Shaheed Nasarallah