Tawagar Iran a Beirut ta gana da shugabannin Lebanon
Published: 24th, February 2025 GMT
Tawagar gwamnatin Iran da ke ziyara a birnin Beirut domin halartar jana’izar shugabannin gwagwarmaya Sayyed Hassan Nasrallah da Sayyed Hashem Safieddine karkashin jagorancin shugaban majalisar dokokin kasar Mohammad Bagher Ghalibaf da ministan harkokin wajen kasar Abbas Araghchi sun gana da shugaban kasar Labanon Joseph Aoun.
Bayan nan kuma tawagar ta gana da shugaban majalisar dokokin kasar Nabih Berri, sannan ta ci gaba da tattaunawa da sauran jami’ai da suka hada da firaministan kasar Labanon Nawaf Salam.
Ghalibaf da sauran jami’ai sun tafi kasar Lebanon a safiyar Lahadi don halartar jana’izar Sayyid Hassan Nasrallah, tsohon babban sakataren kungiyar Hizbullah, da kuma magajinsa Sayyed Hashem Safieddine, wadanda gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kashe su a karshen shekarar da ta gabata.
Da yake zantawa da manema labarai gabanin tafiyar tasa, Ghalibaf ya bayyana jana’izar a matsayin wani lokaci mai ma’ana ga kungiyar gwagwarmaya, duniyar musulmi, da kuma al’ummar Lebanon.
A lokacin da ya isa birnin Beirut babban jami’in na Iran ya bayyana Nasrallah a matsayin wani mutum mai babban matsayi kuma abin alfahari ga duniyar musulmi, yana mai jaddada abin da ya bari a matsayin wata alama ta tsayin daka a kan yakin kisan kare dangi na “Isra’ila” a Gaza.
Ghalibaf ya kara da cewa, duk da shahadarsu, amma Hizbullah da al’ummar Lebanon na alfahari da wadannan gwaraza.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
An rantsar da shugabannin ƙananan hukumomi 34 na Katsina
A wannan Litinin ɗin ce ne aka rantsar da sabbin shugabannin ƙananan hukumomi 34 na Jihar Katsina waɗanda aka gudanar da zaɓensu a ranar 15 ga watan Fabrairu, 2025.
Babban Jojin Jihar Katsina, Mai Shari’a Musa Danladi Abubakar ne ya jagoranci rantsar da sabbin shugabannin ƙananan hukumomin.
’Yar shekara 66 ta haifi ɗanta na 10 da kanta Bello Turji ya kashe manoma 11 a SakkwatoSai dai gab da lokacin da za a rantsar da su, ɗaya daga cikinsu ya faɗi ya sume a lokacin da yake ƙoƙarin shiga rumfar da aka tanadar masu.
Shugaban Ƙaramar Hukumar Bakori Honarabil Aminu Ɗan Hamidu shi ne wanda ya faɗi kuma aka ɗauka ranga-ranga zuwa asibiti.
Binciken da muka yi ya nuna cewa, shugaban ya take wani sashe na babbar rigar shi ne ba tare da ya yi la’akari ba yayin da ya yunƙura da ƙarfi don hawa matattakalar shiga rumfar, lamarin da ya janyo rigar ta shaƙe shi ya faɗi a sume.