Hamas ta yaba da irin goyon bayan da Sayyed Nasrallah ya baiwa Falasdinu
Published: 24th, February 2025 GMT
Kungiyar Hamas ta jinjina da irin babbar gudunmawa da tsayin dakan da Sayyed Hassan Nasrallah da Sayyed Hashem Safieddine suka yi wajen goyon bayan Palastinu, da kuma shahadar da suka yi a kan wannan tafarki.
A cikin wata sanarwa da ta fitar dangane da jana’izar shahidan biyu, kungiyar Hamas ta ce, muna addu’ar Allah ya jikan su da rahama, tare da mika ta’aziyyarmu ga al’ummar kasar Labanon da dukkanin al’ummar mu Larabawa da musulmi.
Kungiyar ta tabbatar da cewa, laifuffukan Haramtacciyyar Kasar Isra’ila da kuma kisan gillar da ta yi wa shugabannin gwagwarmaya a Falasdinu, Labanon da sauran su, ba za su dakatar da tafarkinmu ba.
Har ila yau sanarwar ta bayyana matsayin shahid Sayyid Hassan Nasrallah da jajircewarsa da kuma sadaukar da kai ga al’ummar Palastinu, tare da yabawa kudurinsa na kafa wata hanya ta taimakawa da kuma goyon bayan al’ummar Gaza wajen tinkarar mummunan zaluncin yahudawan sahyoniyawan.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kasashen Larabawa Na Yankin Tekun Farisa Sun Yi Fatan Al-Khairi Ga Iran Da Amurka A Tattaunawar Shirin Nukliyar Kasar
Babban sakataren kungiyar kasashen Larabawa na yankin tekun Farisa (PGCC) ya yi fatan alkhairi ga kasashen Iran da Amurka a tattaunawa ba kai tsaye ba a tsakaninsu dangane da shirin Nukliya ta kasar Iran na zaman lafiya wanda suka fara, a birnin Mascat na kasar Omman a ranar Asabar da ta gabata.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Jasem Mohamed AlBudaiw yana fadar haka a jiya Lahadi ya kuma kara da cewa, kungiyar tana bukatar gidan an warware matsaloli tsakanin kasashen duniya ta hanyar tattanawa. Haka ma tsakanin kasashen yankin.
AlBudaiw ya yabawa kasar Omman da shirya wannan tattaunawar, sannan ya yi fatan tattaunawan da aka fara zai kai ga rage tada jijiyoyin wuya a yankin da kuma kasashen duniya, ya kuma ce kasashen yankin suna fatan zasu kai ga sakamako mai kyau tsakanin kasashen biyu.
Gwamnatin kasar Iran dai tana har yanzun suna shakkar kasar Amurka saboda yawan yaudarar da tayiwa kasar a baya. Musamman fitar kasar daga yarjeniyar JCPOA a shekara ta 2018. Da kuma yawan takunkuman da ta dorawa a kasar tun lokacin.
Daga karshe babban sakataren kungiyar ta PGCC ya ce tana fatan za’a kawo karshen duk wani rikici a gabas ta tsakiya daga ciki har da na HKI a falasdinawa a Gaza ta hanyar tattaunawa da fahintar Juna.