Nan Kusa Ƴan Majalisun NNPP Za Su Koma APC – Ganduje
Published: 24th, February 2025 GMT
Nan Kusa Ƴan Majalisun NNPP Za Su Koma APC – Ganduje .
এছাড়াও পড়ুন:
Hakuri Da Biyayya Su Ne Sirrin Ɗaukaka A Masana’antar Kannywood – Mu’azu
Daga karshe, jarumin wanda ya shafe shekaru fiye da 10 a Masana’antar Kannywood, ya shawarci matasa masu sha’awar shiga harkar fim, su tabbatar sun zama masu hakuri da biyayya ga na gaba da su, muddin suna son samun nasara a rayuwarsu ta jarumai.
“Dole ne ka kasance mai hakuri a rayuwa, domin kuwa babu wanda ya zama wani abu ba tare da ya sanya hakuri a cikin al’amuransa na yau da kullum ba, duk wanda ka gani ya zama wani abu, ko ya samu wata daukaka ko shahara a rayuwa, to dole akwai kalubalen da ya fuskanta, domin kuwa ko a makaranta sai an ware wani lokaci da za a yi jarrabawa; domin gane masu fahimta da wadanda ba sa fahimta”.
Haka zalika, dole ne ka kasance mai biyayya a duk inda ka samu kanka, muddin kana so kai ma wata rana a yi maka biyayya, musamman a masana’anta irin ta Kannywood, duk manyan jarumai irin su Ali Nuhu, Hadiza Gabon da sauran makamatansu; sai da suka yi biyayya, suka kuma yi hakuri kafin su kai matsayin da suke kai yanzu, in ji Muhammad.