Kasashen Sin da Afirka ta Kudu sun kara zurfafa alakar da ke tsakanin juna
Published: 24th, February 2025 GMT
A yayin taron ministocin harkokin wajen kasashen G20 da aka yi a birnin Johannesburg, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi da takwaransa na Afirka ta Kudu Ronald Lamola sun yi wata ganawa ta musamman, inda suka tattauna dangantakar kasashensu da manufofinsu.
Sun amince da manufa guda don habaka tasirin Duniya, da nufin tabbatar da ingantacciyar murya guda ta kasashe masu tasowa.
Wang ya bayyana a yayin taronsu cewa, kasar Sin a shirye take ta kara karfafa hadin gwiwar cin moriyar juna tsakaninta da kasar Afirka ta kudu, da kara gaggauta bunkasuwar kasashen biyu, da kuma kara yin hadin gwiwa don kara daukaka murya da wakilci na kasashe masu tasowa, musamman kasashen Afirka a cikin ajandar kasa da kasa.
Wannan tattaunawar ta faru ne a wani muhimmin lokaci a yayin da ake gudanar da taron ministocin harkokin wajen kasashen G20 a birnin Johannesburg na Afirka ta kudu, inda aka baiwa kasashen biyu damar karfafa kawance da ba da shawarar yin tasiri a shawarwari na kasa da kasa.
All Posts
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kamata Ya Yi Amurka Ta Kara Kokarin Gyara Kuskurenta
Wasu kafofin yada labarai a duniya na ganin cewa, idan gwamnatin Amurka ta ci gaba da saka shingayen haraji, to sauran kasashe za su maye gurbinta a bangaren samar da hidimomi. Abin da gwamnatin ta yi biris da shi yayin da take kididdigar harajin da za ta kakabawa sauran sassa, har yanzu wannan bangare na shiga gogayyar ciniki.
Bisa bayyanan da aka fitar, Amurka ta dade tana cin rarar kudin ciniki a bangaren ba da hidimomi. Alal misali a shekarar 2024, yawan rarar kudin da ta samu a wannan bangare ya kai dala biliyan 300. Kuma Abin lura shi ne, cinikin hidimomi na matukar dogaro da cinikin kayayyaki. Gibin kudin cinikin da Amurka ta samu a bangaren cinikin kayayyaki da rarar kudin cinikin da ta samu ta fuskar cinikin hidimomi, ya faru ne bayan sauyin salon sana’o’i bisa matakai daban daban, ta yadda suka kasance tagwaye da ba za a iya raba su ba.
Idan an yi waiwaye kan tushen cinikin hidimomi wato batun amincewa, a wadannan shekaru da suka gabata, Amurka ta rika sanya takunkumai da haifar da barazana ga dukkanin fadin duniya, wanda hakan ya rage kimarta, da amincewa daga sauran kasashe. A halin yanzu, Amurka ta kakabawa sauran kasashe harajin kwastam yadda take so, kuma abun tambaya shi ne wa zai karbi hidimomin da Amurka za ta samar a bangaren hada-hadar kudi, da ba da ilmi da bayanai da kuma kwamfuta?
Amurka ita kanta za ta dau laifin gogayyar ciniki, matakin da ta dauka a wannan karo na kawar da harajin kwastam na ramuwar gayya kan wasu kayayyaki, dabara ce ta kubutar da kanta daga mawuyacin hali. Amma, hakan bai wadatar ba, dole ne ta dauki karin matakai na soke dukkanin wannan haraji da ta kakabawa sauran kasashe. A wani bangare kuwa, ta mutunta abokan cinikinta, ta yi shawarwari da su bisa adalci da daidaito, a matsayin hanya daya tilo mafi dacewa da za ta bi wajen warware bambancin ra’ayi na ciniki. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp