Ƴansanda Sun Daƙile Harin Ƴan Bindiga Kan Jami’an NSCDC A Katsina
Published: 24th, February 2025 GMT
Rundunar ‘yansandan Jihar Katsina ta hana wani yunƙurin ‘hari da ‘yan bindiga suka kai kan jami’an NSCDC a kan hanyar Dutsinma-Kurfi a ƙaramar hukumar Dutsinma.
Kakakin rundunar, DSP Abubakar Sadiq Aliyu, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da sanyin safiyar Lahadi, 23 ga Fabrairu, 2025. Bayan samun kiran gaggawa da misalin ƙarfe 12:57 na dare, ‘yansanda daga ofishin Dutsinma suka gaggauta kai ɗauki, wanda ya haifar da musayar wuta da ‘yan bindigar.
A sakamakon haka, ‘yan bindigar sun tsere da raunukan harbin bindiga, yayin da aka samu gawar ɗaya daga cikinsu a wurin. Jami’an tsaro sun ƙara ƙaimi wajen bin sawun waɗanda suka tsere domin cafke su.
Rundunar ‘yansandan ta tabbatar da ci gaba da jajircewarta wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma a fadin jihar.
এছাড়াও পড়ুন:
MDD Ta Nuna Damuwarta Akan Kokarin Sake Raba Kasar Sudan Gida Biyu
Mai Magana da yawun kakakin babban magatakardar MDD Steven Dujarric ya nuna damuwa akan sanar da kafa wata gwamnati ta daban da shugaban rundunar daukin gaggawa Hamidati Duklu ya yi a shekaran jiya Laraba.
Shugaban rundunar kai daukin gaggawar ta Sudan wanda yake fada da sojojin kasar ya shelanta kafa sabuwar gwamnati wacce ya ce za ta kasance ta zaman lafiya da hadin kai ce.
Hamidati wanda ya gabatar da jawabi a lokacin da ake tunawa da zagayowar cikar shekaru 3 da fara yaki a kasar ta Sudan, ya kuma ce; A halin yanzu suna Shirin buga kudaden Sudan na daban, da kuma samar da wasu muhimman takardu na aikin gwamnati.
Wannan sanarwar daga shugaban rundunar kai daukin gaggawar ta Sudan yana zuwa ne bayan da sojojin Sudan su ka kori mafi yawancin mayakansa daga birnin Khartum da kuma wasu muhimman wuraren a kasar ta Sudan.
A watan da ya shude ne dai shugaban dakarun kai daukin gaggawa na Sudan din ya halarci wani taro a kasar Kenya da ya shelanta kafa gwamnatin bayan fage tare da wasu kungiyoyi da suke goya masa baya.
Shi dai Hamidati yana fuskantar zarge-zarge daga kungiyoyin kare hakkin bil’adama na kasa da kasa akan aikata laifuka da su ka hada da yi wa mata fyade da cin zarafin kananan yara.