Iran na da niyyar kara karfafa alakarta da kasashen Afirka
Published: 24th, February 2025 GMT
Pars Today – Mataimakin shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya sanar da cewa za a gudanar da taron hadin gwiwar tattalin arziki tsakanin Iran da Afirka karo na uku da kuma bikin baje kolin na shekarar 2025 a farkon shekara mai zuwa wato (Kalandar Iran).
Mataimakin shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran Muhammad Reza Aref, a wata ganawa da ya yi da shugabannin jami’an diflomasiyyar Afirka a birnin Tehran ya bayyana cewa, raya dangantakar tattalin arziki da cinikayya da nahiyar Afirka, na daya daga cikin muhimman batutuwan da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta sanya a gaba.
Aref ya kara da cewa, shirya taron hadin gwiwar tattalin arziki tsakanin Iran da Afirka karo na uku da kuma bikin baje kolin na shekarar 2025 a farkon shekara mai zuwa wato (Kalandar Iran) na cikin ajandar gwamnati ta 14 a Iran.
Aref ya jaddada cewa, bunkasa cikakken hadin gwiwa tare da nahiyar Afirka a fannin tsare-tsare tsakanin bangarorin biyu, da sauran bangarori daban-daban, shi ne fifiko ga Iran, yana mai cewa: Idan aka yi la’akari da irin karfin da bangarorin biyu suke da shi, yin hadin gwiwa da tattara dukkan albarkatu da karfinsu, to za su iya ba da gudummawa sosai ga ci gaban dangantaka da hidima ga jama’arsu.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kasashen Iran Da Katar Sun Jaddada Muhimmancin Shigar Da Dukkanin Bangarorin Al’ummar Kasar A Cikin Sha’anin Kasar
Manzon musamman na ministan harkokin wajen Iran a kan Syria, Muhammad Ridha Ra’uf Shaibani ya gana da karamin minista a gwamnatin kasar Katar inda su ka tattauna halin da ake ciki a kasar Syria, haka nan kuma sun jaddada wajabcin shigar da dukkanin bangarorin al’ummar kasar a cikin sha’anin tafiyar da gwamnati.
A jiya Laraba ne dai Muhammad Ridha Shaibani ya kai ziyara birnin Doha inda ya gana da ministan na kasar ta Katar Muhammad al-Khalifi domin yin shawara akan Syria.
Shaibani ya bayyana mahangar Iran akan Syria, da ya kunshi ganin an shigar da kowane bangare na al’ummar kasar a cikin sha’anin tafiyar da kasar, ya kuma zama sun taka rawa wajen ayyana makomar kasar.
A nashi gefen ministan na kasar ta Katar Muhammad al-Khalifi ya yi ishara da rawar da Iran take takawa a cikin wannan yankin da kuma tasirisnta, haka nan kuma ya bayyana wajabcin ci gaba ta tuntubar juna domin musayar ra’ayi akan halin da kasar ta Syria take ciki.
Haka nan kuma bangarorin biyu sun tattauna hanyoyin bunkasa alaka a tsakanin kasashensu.