HausaTv:
2025-03-28@04:30:33 GMT

Al-Khazali: ‘Yan gwagwarmaya a Iraki za su gaba da bin tafarkin Sayyid Nasrallah

Published: 24th, February 2025 GMT

Dakarun gwagwarmaya a Iraki za su ci gaba da ayyuka bisa tafarkin babban sakataren kungiyar Hizbullah Sayyid Hasan Nasrallah, wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen kare wadanda ake zalunta, kamar yadda Qais al-Khazali, babban sakataren kungiyar Asa’ib Ahl al-Haq ya bayyana.

Da yake magana a ranar wannan Lahadin, al-Khazali ya jinjinawa Sayyed Nasrallah, yana mai bayyana shi a matsayin babban mutum wanda ya shafe tsawon rayuwarsa a tafarkin jihadi da kare wadanda ake zalunta.

Ya kara tabbatar da cewa babu makawa wa’adin Sayyed Nasrallah na samun nasara a kan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila yana zuwa.

“Mun yi alkawarin shrda ma Nasrallah cewa, za mu ci gaba da tafiya a kan wannan tafarki har zuwa lokacin da za a tsarkakae kasar Falastinu daga mamayar  gwamnatin Haramtacciyar kasar Isra’ila da yahudawan sahyuniya, in ji shi.

A cewar Hani Khater, shugaban ofishin yada labarai na Al-Ahed na kasar Iraki a ofishin Tehran, kimanin ‘yan kasar Iraki dubu 200 ne suka halarci jana’izar Sayyed Nasrallah a jiya Lahadi a birnin Beirut.

Sannan kuma Ya yi nuni da cewa, akidar Sayyed Nasrallah za ta ci gaba da dawwama a duk fadin yankin gabas ta tsakiya da ma duniya baki daya.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: Sayyed Nasrallah

এছাড়াও পড়ুন:

Kamfanin BYD Ya Samu Karin Ribar Kaso 34 Zuwa Dala Biliyan 5.6 A Bara

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  •  Sojojin Iran: Gwagwarmaya Ce Kadai Hanyar Warware Matsalar Falasdinu
  • Iran, Lebanon, Iraki, Yemen sun fara atisayen hadin gwiwa na goyan bayan Gaza
  • Isra’ila ta sake kashe wani kakakin Hamas
  • Hukumar IAEA ta yi ishara da yiwuwar sake komawa teburin tattaunawa tare da Iran
  • Kamfanin BYD Ya Samu Karin Ribar Kaso 34 Zuwa Dala Biliyan 5.6 A Bara
  • Kasuwar Kayayyakin Masarufi Ta Sin Za Ta Ci Gaba Da Nuna Yanayin Bunkasa Bisa Daidaito A Bana
  • Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Ya Ce Zargin Kasar Amurkan Dangane Da Kamfanonin Man Fetur Na Kasar Ba Gaskiya Bane
  • Yansanda A Kasar Turkiyya Suna Ci Gaba Da Fafatawa Da Yan Adawa A Birnin Istambul
  • Lauyoyi 77 a Jamus sun yi kira ga gwamnati da ta mutunta sammacin ICC na cafke Netanyahu
  • Dakarun Yemen sun kara kai hare-hare goyan bayan Falasdinu