Iran ta yi Allah wadai da keta hurumin kasar Lebanon da Isra’ila ta yi
Published: 24th, February 2025 GMT
Iran ta yi kakkausar suka kan ta’addancin Isra’ila game da keta hurumin kasar Lebanon, bayan da jiragen yakinta suka yi shawagi a yankin da ake gudanar da jana’izar tsoffin shugabannin kungiyar Hizbullah.
A wani sako da ya wallafa a shafin sada zumunta a daren Lahadi, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Esmaeil Baghaei, ya ce gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta shiga wani sabon yanayi na kara tabbatar wa duniya da cewa ita bata bin dokokin kasa da kasa.
Baghaei ya ce jiragen yakin haramtacciyar kasar Isra’ila sun yi kokarin tarwatsa dubban daruruwan ‘yan kasar Lebanon da wasu da suka taru domin nuna girmamawa ga jarumtansu, shugaban kungiyar Hizbullah Sayyed Hassan Nasrallah da mataimakinsa da suka nada Sayyed Hashem Safieddine.
Baghaei ya yi kira ga kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ya yi Allah wadai da wannan mataki na rashin da’a, da rashin girmamam dokokin duniya da Isra’ila ta nuna a jiya a lokacin janazar Sayyid Hassan Nasrullah a Beirut.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Iran Ta Turkiyya Sun Bukaci kasashen Musulmi Su Magance matsalar Jinkai A Kasar Palasdinu Da Aka Mamaye
A zantawa ta water tarho ministocin harkokin waje na kasashen Iran da Turkiya sun bukaci kasashen musulmi su magance matsalar jinkai da kayakin agaji na Falasdinawa a kasarsu da aka mamaye.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Hakan Fidan na kasar Turkiya da tokwaransa na kasar Iran Abbas Aragchi suna fadar haka a jiya Litinin.
A lokacinda yake Magana a kan rikicin da ke faruwa a kasar Turkiyya Abbas Aragchi ya bayyana cewa, rikici ne na cikin gida, kuma yana fatan gwamnatin kasar zara iya magancece ta yadda ta ga ya dace, kuma yana da imani zata iya magance matsalar.
Aragchi ya kara da cewa, wannan shi ne matsayin iran a cikin al-amuran da ke faruwa a kasashen yankin, ya kuma bayyana muhimmancin mutunta al-amuran da suka shafi cikin gida na ko wace kasa a yankin.
Sai kuma Hakan Fidan ministan harkokin wajen Turkiya wanda ya sake jadda matsayin kasarsa wajen neman hanyoyin diblomasiyya don warware matsalolin al-amuran Falasdinu da kasashen yankin da kuma sauran kasashen duniya.