Gwamnatin Jigawa Ta Bada Aikin Gyaran Titin Birnin Kudu Akan Kudi Naira Biliyan 11.5
Published: 24th, February 2025 GMT
Gwamnatin jihar Jigawa ta bayyana jin dadinta bisa gagarumin nasarorin da aka samu wajen aiwatar da manufofinta guda 12 don inganta rayuwar al’umma da ma ci gaban jihar baki daya.
Gwamna Umar Namadi ya bayyana hakan a yayin taron wayar da kan jama’a da aka gudanar a karamar hukumar Birnin Kudu.
Ya bayyana cewa shirin da ke da nufin kusantar da jama’a ga gwamnati, zai kuma tabbatar da cewa manufofi da shirye-shiryen da aka aiwatar sun dace da muradin al’umma.
Don haka Namadi ya yabawa al’ummar yankin bisa yadda suka rungumi ayyukan da gwamnatin jihar ke aiwatarwa hannu bibbiyu, tare da yin alwashin ci gaba da samar da ingantattun ayyuka.
Gwamnan ya kuma ba da tabbacin cewa, zai yi nazarin takardar da Farfesa Abubakar Sani Birnin Kudu ya gabatar mai kunshe da bukatun al’ummar karamar hukumar ta Birnin Kudu.
Shi ma da yake jawabi kwamishinan ayyuka da sufuri na jihar Injiniya Gambo S. Mallam ya ce gwamnatin jihar ta bada kwangilar sake gina hanyar Birnin Kudu zuwa Sundimina zuwa Kiyawa, akan kudi naira biliyan 11 da miliyan 500.
A cewarsa, aikin zai hada da sanya kwalta, da gina gadoji da magudanan ruwa, da sauran abubuwan da suka kamata.
Injiniya Gambo ya yi nuni da cewa, a halin yanzu gwamnatin jihar na gudanar da ayyukan tituna da dama a karamar hukumar Birnin Kudu.
Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa, gwamnan farar hula na farko a jihar Alhaji Ali Sa’ad Birnin Kudu ne ya kaddamar da aikin sake gina hanyar ta Birnin Kudu zuwa Sundimina, zuwa Kiyawa a hukumance.
Usman Muhammad Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Jigawa
এছাড়াও পড়ুন:
Araghchi: babu tattaunawa kan batun tace sinadarin uranium
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa babu batun tattaunawa kan shirin kasar na tace sinadarin Uranium wanda ke a matsayin wani bangare na shirin nukiliyar kasar na zaman lafiya.
Abbas Araghchi ya kuma ce tattaunawar Tehran da Washington ba za ta haifar da wani sakamako ba idan ana amfani da matsin mata lamba da rashin mutunta juna.
Mista Araghchi ya bayyana hakan ne a gefen taron majalisar ministocin gwamnatin Iran na mako-mako a birnin Tehran babban birnin kasar, bayan da manzon musamman na Amurka Steve Witkoff ya ce Tehran “dole ne ta kawar da” shirinta na inganta makamashin nukiliya domin cimma matsaya da Washington.
Kalaman na zuwa ne a daidai lokacin da bangarorin ke shirin ganawa a ranar Asabar.
Da ya tabo yunkurin da Amurka ke yi na matsin lamba kan Iran a yayin shawarwarin, ministan harkokin wajen na Iran ya ce: Matsayinmu da ayyukanmu a bayyane suke, ba za su cimma komai ta hanyar matsin lamba ba, idan aka yi shawarwarin a cikin yanayi na mutuntawa, za a iya samun ci gaba, amma babu abin da za a samu ta hanyar matsin lamba ba.
Araghchi ya kuma soki “wasu batutuwa masu cin karo da juna” da ke fitowa daga gwamnatin Trump gabanin tattaunawar ta ranar Asabar.
Dama tun farko Jagoran juyin juya halin musulinci na Iran, Ayatullah Khamenei ya bayyana a ranar Talata cewa tattaunawar Iran da Amurka a birnin Muscat na kasar Omani ta yi kyau a matakin farko, sai dai ya kara da cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana da matukar shakku ga daya bangaren.