Galadima Muri, na Masarautar Muri, kuma Hakimin Jalingo, Alhaji Lamido Abba Tukur, ya yi kira ga manoma da ‘yan kasuwa a Taraba da su yi la’akari da halin da talakawa ke ciki, su rage farashin kayan abinci.

Ya yi wannan kiran ne a yayin cikarsa shekaru 40 akan karagar mulki a matsayin Galadima a Jalingo.

Basaraken  ya nuna damuwarsa kan yadda hauhawar farashin kayayyakin abinci a kullum ke kara ta’azzara, da kuma kalubalen tattalin arziki da talakawa ke fuskanta.

Galadiman ya yabawa gwamna Agbu Kefas kan yaki da matsalar tsaro a Taraba, inda ya bayyana ci gaban da aka samu a shekarun baya-bayan nan a matsayin abin a yaba.

“Amincewa da gudanar da wannan biki na cika shekara 40 akan karagar mulki a matsayin Galadima a yau, ya biyo bayan yakin da Gwamna Kefas ya yi da wajen tabbatar da ganin an shawo kan matsalar tsaro a Taraba, tare da wanzar da zaman lafiya, ba a Jalingo kadai ba, har ma a jihar Taraba baki daya, wanda ya baiwa jama’a damar samun hanyoyin samun kudaden shiga na yau da kullum“. Inji shi.

“A matsayina na babasaranaina shiga cikin damuwa matuka a duk lokacin da jama’ata suka gaza shiga gonakinsu ko gudanar da  sana’o’insu saboda rashin tsaro. Ina son in yaba wa gwamna Agbu Kefas bisa gaggarumin yaki da rashin tsaro a Taraba, wanda sannu a hankali ana samun kwanciyar hankali a halin yanzu.

Tun da farko, shugaban taron, Alhaji Kabiru Marafa, da Lamido Bakundi, mai martaba Alhaji Kabiru Muhammad Gidado Misa, sun bayyana Galadima a matsayin basarake abin koyi, wanda ake alfahari da ayyukansa da jagororinsa.

Jamila Abba

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Kasar Pakistan Ta Kara Jaddada Dokar Rashin Amincewa Da HKI A Matsayi Kasa

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Pakisatan ta kara jaddada matsayinta na rashin amince da HKI a matsayin kasa tana kuma goyon bayan Falasdinawa a gwagwarmayan da suke yi na kwatar yencinsu da kuma kasarsu daga hannun HKI da kuma kasashen yamma musamman Amurka masu goya mata.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran wannan sanarwan tazo ne bayan da hukumar kare hakkin bil’adama ta MDD ta samar da wani kuduri dangane da rikicin da ke faruwa a gabas ta tsakiya.   A dai-dai lokacinda aka kara yawan tashe-tashen hankula a kasar Falasdinu da aka mamaye tsakanin HKI da kuma Falasdinawa masu gwagwarmaya. Kungiyar kasashe masu musulmi mafi rinjaye wato OIC ta yanke  shawara kan cewa bai kamata kasashen su samar da huldar Diblomasiyya da HKI ba.  Ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Pakisatn ta bayyana cewa, kafafen yada labarai da dama sun watsa labaran cewa kasar ta Canza matsayinta dangane da kudurin hukumar kare hakkin bil’adama ta MDD dangane da rikicin nag abas ta tsakiya, ta kuma kara da cewa wannan labarin ba gaskiya bane. Saboda kasar Pakistan tana tare da kungiyar OIC dangane da goyon bayan al-ummar Falasdinu. Don haka Pakisatan bata amincea da samuwar HKI ba. Har’ila yau majalisar kasa ta kasar Pakisatn ta amince da babban rinjaye ko kuma gaba dayan yan majalisar da rashin amincea da HKI da kuma goyon bayan Falasdinawa.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kasar Pakistan Ta Kara Jaddada Dokar Rashin Amincewa Da HKI A Matsayi Kasa
  • An Yi Kira Ga Jihohi Da Su Kara Samar Da Ingantacciyar Hanyar Kiyon Lafiya
  • Matatar Dangote Ta Sake Rage Farashin Man Fetur Zuwa N835 Kan Kowace Lita
  • ‘Yan Bindiga Sun Kashe Manoma 7 A Wani Sabon Hari A Benuwe
  • Samarwa Matasa Abun Yi Shi Zai Kawo Ƙarshen Ta’addancin Boko Haram Da ‘Yan Bindiga – Zulum 
  • Gwamnatin Jigawa Ta Bukaci Jami’an Tsaro Mata Su Rika Sanya Hijabi Yayin Aiki
  • Ina Dalilin Da Ya Sa Cinikin Shige Da Fice Na Kasar Sin Ke Samun Bunkasuwa Mai Dorewa Ba Tare Da Tangarda Ba?
  • Shugaba Xi Ya Yi Kira Ga Sin Da Vietnam Da Su Wanzar Da Daidaito A Tsarin Rarraba Hajoji
  • ‘Yansanda Sun Kama Wani Kato Bisa Zargin Cin Zarafin Wata Mata A Adamawa
  • ’Yar shekara 66 ta haifi ɗanta na 10 da kanta