Radio Nigeria Kaduna Hausa:
2025-03-28@03:16:16 GMT

Sojojin Sudan Sun Kace Birnin El-Obeid Daga Hannun RSF

Published: 24th, February 2025 GMT

Sojojin Sudan Sun Kace Birnin El-Obeid Daga Hannun RSF

Sojojin Sudan sun ce sun kawo ƙarshen iko da birnin el-Obeid na yankin kudancin ƙasar na kusan shekaru biyu da dakarun RSF suka yi.

Wannan nasara na zuwa ne ‘ƴan sa’o’i bayan da RSF ta rattaɓa hannu kan yarjejeniyar siyasa a Nairobi da ke ƙasar Kenya na kafa gwamnatin aware a yankunan da ke ƙarƙshin ikonta.

Tun dai shekarar 2023 ne rundunar RSF da sojojin Sudan ke fafatawa, inda dubban fararen hula ke mutuwa sannan da dama na barin gidajensu.

Rikicin dai ya raba ƙasar ɓangarori biyu, inda sojoji ke iko da arewa da gabashi, yayin da su kuma RSF ke iko da mafi yawancin yankin Darfur da ke yammaci da wasu sassan kudanci.

Birnin El-Obaid dai wanda shi ne babban birnin jihar Kordofan, yana da matuƙar muhimmanci ga Khartoum, babban birnin ƙasar. Wannan ne wani yunƙuri na sojoji a ƴan makonnin nan tun bayan kame yankuna da dama na Khartoum daga hannun RSF.

Al’ummar Sudan sun fito tituna suna ta bayyana farin cikinsu dangane da sake ƙwato birnin daga hannun waɗanda suke bayyanawa a matsayin ƴan tawaye.

Wata mai fafutuka ƴar ƙasar Sudan, Dallia Abdlemoniem ta shaida wa BBC cewa ƙwace iko da birnin daga hannun RSF “gagarumar” nasara ce.

Ta ƙara da cewa sojoji na ci gaba da shirin kutsawa yammaci inda a can ne mayaƙan na RSF suke.

Dukkannin ɓangarorin biyu na sojojin gwamnati da na rundunar mayaƙan RSF sun musanta zarge-zargen take haƙƙin bil’ada da aka yi musu, da har ta kai Amurka ta ƙaƙaba wa jagororinsu takunkumai. Bugu da ƙari, an zargi RSF da aikata laifukan kisan ƙare dangi a Darfur.

An soki ƙasar Kenya bisa karɓar ɓakuncin da ta yi makon da ya wuce da ke son kafa gwamnatin ƴan aware.

Da ma dai gwamnatin sojin Sudan ta gargaɗi Kenya da cewa za ta yi ramuwar gayya kan Kenyar bisa matakin, kuma tuni ta yi wa jakadanta da ke Nairobi kiranye.

Sai dai a wani martani da suka yi, ministan harkokin wajen Kenya ya ce babu “wata mummunar manufa” a “bai wa dukkan ɓangarorin da ke rikici da juna dama.

bbc

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

An Ɗauko Sojoji Daga Waje Don Horas Da Dakarun Nijeriya 

A yankunan kamar Birnin Gwari a Kaduna, ana samun ci gaba bayan ƙarin matakan tsaro da aka ɗauka.

Gwamnati na fatan wannan horo zai taimaka wajen rage hare-haren ‘yan bindiga, ceto mutanen da ake garkuwa da su, da kuma kawo ƙarshen rashin tsaro a yankunan da ke fama da matsalar.

Ana sa ran wannan shiri zai ƙara inganta ƙoƙarin jami’an tsaro, domin daƙile hare-haren da ake yawan kai wa a yankin Arewa da wasu sassan Nijeriya.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sojojin Sudan Suna Ci Gaba Da Samun Nasara A Akan Dakarun Kai Daukin Gaggawa
  • An kama mataimakin shugaban Sudan ta Kudu
  • Sudan : Janar al-Burhan Ya Shelanta ‘yantar Da Birnin Khartoum
  •  Nigeria: An  Kashe Sojoji Da DAma A Wani Hari Da Aka Kai Wa Sansanonin Soja Biyu Hari A Jihar Borno
  •  Sojojin Sudan Sun Kwace Wuri Na Karshe Da Yake A Hannun “Rundunar Kai Daukin Gaggawa” A Cikin Birnin Khartum
  • Boko Haram Ta Kashe Sojoji A Wani Sabon Hari A Borno
  • Sudan: RSF ta hana kayan agaji a yankunan da ke a karkashin ikonta
  • Yansanda A Kasar Turkiyya Suna Ci Gaba Da Fafatawa Da Yan Adawa A Birnin Istambul
  • Za mu ɗauko hayar sojojin ƙetare domin horas da dakarun Nijeriya — Badaru
  • An Ɗauko Sojoji Daga Waje Don Horas Da Dakarun Nijeriya