NNPP ta dakatar da Kawu Sumaila da Ali Madakin Gini
Published: 24th, February 2025 GMT
Jam’iyyar NNPP a Kano ta dakatar da Sanata Kawu Sumaila da wasu ƙusoshin jam’iyyar uku kan zargin cin amanarta.
Sauran waɗanda jam’iyyar kan zargin cin amana sun haɗa da Ali Madakin Gini, Sani Abdullahi Rogo da kuma Kabiru Alhassan Rurum.
.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Jihar Kano Kawu Sumaila
এছাড়াও পড়ুন:
Yau Kotun ICJ ke yanke hukunci kan zargin da Khartoum ke wa UEA
Yau Litinin ne kotun kasa da kasa ta ICJ za ta yanke hukunci kan karar da Sudan ta shigar kan Hadaddiyar Daular Larabawa.
Khartoum ta kai karar UAE a gaban kotun kasa da kasa da ke birnin Hague, inda ta zarge ta da hannu wajen kisan kiyashin da ake yi wa al’ummar Masalit, sakamakon zarginta da goyon bayan dakarun (RSF) da suka shafe shekaru biyu suna yaki da sojojin Sudan.
Khartoum na zarginsu da kasancewa masu goyan bayan kisan kare dangi” da ake ci gaba da yi wa al’ummar Massalit na Darfur, saboda zarginsu da goyon bayan dakarun gaggawa na Janar Hemedti (RSF).
Khartoum na fatan alkalan kotun su umurci Hadaddiyar Daular Larabawa da ta daina goyon bayan kungiyar RSF, da kuma cewa suna bukatar ta biya “diyya” ga wadanda rikicin ya rutsa da su.
Rahotanni da dama daga kungiyoyi masu zaman kansu da kwararru na Majalisar Dinkin Duniya sun yi nuni da goyon bayan da Hadaddiyar Daular Larabawa ke baiwa kungiyar RSF, musamman ta hanyar shigar da makamai.
Amma Masarautar ta musanta hannu a wannan rikicin.
rikicin na Sudan da ke gudana tun a ranar 15 ga Afrilu, 2023 tsakanin sojoji na yau da kullun, karkashin jagorancin Abdel Fattah al-Burhan, da FSR, karkashin jagorancin tsohon mataimakinsa Mohamed Hamdane Dogolo, wanda aka fi sani da “Hemedti,” ya yi sanadin mutuwar dubunnan mutane a Sudan, sannan ya raba mutane miliyan 13 da muhallansu, wanda ya haifar da “daya daga cikin mafi munin yanayi a duniya”.