NNPP Ta Dakatar da ‘Yan Majalisa Huɗu Bisa Zargin Yi Wa Jam’iyya Zagon Ƙasa
Published: 24th, February 2025 GMT
Jam’iyyar NNPP reshen jihar Kano ta dakatar da ‘yan majalisar tarayya huɗu bisa zargin aikata abubuwan da suka saɓa wa manufofin jam’iyya. Shugaban jam’iyyar a jihar, Alhaji Hashimu Dungurawa, ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a Kano a ranar Litinin.
Waɗanda aka dakatar sun hada da Kawu Sumaila (Sanatan Kano ta Kudu), Ali Madakin Gini (Dala), Sani Rogo (Rogo/Karaye), da Kabiru Rurum (Rano/Kibiya).
Dungurawa ya ce waɗannan ‘yan majalisa sun samu tikitin NNPP ne, amma daga baya suka fara aikata abubuwan da suka sabawa jam’iyyar.
Ya ce misali, Sanata Sumaila ya ƙaddamar da wasu ayyuka a jami’arsa ba tare da ya gayyaci wakilan jam’iyyar ba, wanda hakan ya nuna alamun yi wa NNPP zagon ƙasa. Shugaban jam’iyyar ya ƙara da cewa za a kafa kwamitin bincike domin tantance lamarin da ɗaukar matakin da ya dace.
Sai dai Dungurawa ya ce har yanzu jam’iyyar na da shirin sasanta matsalar, inda ya bayyana cewa idan waɗanda aka dakatar suka gyara dangantakarsu da jam’iyya, za a iya dawo da su. Wannan matakin na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun rahotannin rikicin cikin gida a NNPP, inda wasu mambobi ke kukan ana ware su daga harkokin jagoranci.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন: