Babbar kotun tarayya da ke Gusau a jihar Zamfara ta dakatar da majalisar dokokin jihar daga tsige Honarabul Aliyu Ango Kagara, dan majalisar APC mai wakiltar mazabar Talata Mafara ta Kudu.

A wata sanarwa da Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar APC na Zamfara, Yusuf Idris Gusau ya fitar, ya bayyana cewa hukuncin ya biyo bayan wata kara mai lamba FHC/GSCS/10/2025 da Kagara ya shigar kan Majalisar Dokokin Jihar Zamfara,  da Kakakinta, da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC).

Ta ce shari’ar da mai shari’a Salim Olasupo Ibrahim ya jagoranta ta kalubalanci tsige Kagara da shugabannin majalisar suka yi.

A cewar sanarwar, kotun ta bayar da umarnin wucin gadi na hana INEC gudanar da zaben cike gurbi na mazabar Talata Mafara ta Kudu, wanda Kagara ke wakilta a halin yanzu.

Mai shari’a Olasupo ya kuma bayar da umarnin tsayawa kan wannan hukunci har zuwa lokacin da za a ci gaba da sauraron karar da aka shigar a gaban kotu.

An dage sauraron karar zuwa ranar 12 ga watan Maris na 2025.

A halin da ake ciki, majalisar dokokin jihar Zamfara ta dakatar da ‘yan majalisa 9 da suka fito daga jam’iyyu daban daban, lamarin da ya rage yawan mambobinta da ke kasa da kashi biyu bisa ukun da ake bukata wajen zartar da kudiri.

Duk wata doka da aka zartar a ƙarƙashin wannan yanayi, ana iya ɗaukarta sabawa tsarin mulki.

 

Daga Aminu Dalhatu

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Majalisar Dokoki Zamfara

এছাড়াও পড়ুন:

Iran ta yi Allah wadai da keta hurumin kasar Lebanon da Isra’ila ta yi

Iran ta yi kakkausar suka kan ta’addancin Isra’ila game da keta hurumin kasar Lebanon, bayan da jiragen yakinta suka yi shawagi a yankin da ake gudanar da jana’izar tsoffin shugabannin kungiyar Hizbullah.

A wani sako da ya wallafa a shafin sada zumunta a daren Lahadi, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Esmaeil Baghaei, ya ce gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta shiga wani sabon yanayi na kara tabbatar wa duniya da cewa ita bata bin dokokin kasa da kasa.

Baghaei ya ce jiragen yakin haramtacciyar kasar Isra’ila sun yi kokarin tarwatsa dubban daruruwan ‘yan kasar Lebanon da wasu da suka taru domin nuna girmamawa ga jarumtansu, shugaban kungiyar Hizbullah Sayyed Hassan Nasrallah da mataimakinsa da suka nada Sayyed Hashem Safieddine.

Baghaei ya yi kira ga kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ya yi Allah wadai da wannan mataki na rashin da’a, da rashin girmamam dokokin duniya da Isra’ila ta nuna a jiya a lokacin janazar Sayyid Hassan Nasrullah a Beirut.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Da Ɗumi-ɗumi: NNPP Ta Dakatar Da Sanata Kawu Sumaila Da Wasu ‘Yan Majalisa Uku
  • NNPP Ta Dakatar da ‘Yan Majalisa Huɗu Bisa Zargin Yi Wa Jam’iyya Zagon Ƙasa
  • Iran ta yi Allah wadai da keta hurumin kasar Lebanon da Isra’ila ta yi
  • Gwamnatin Tarayya Ta Bukaci Al’umma Da Su Rika Taimakawa Hukumomin Tsaro Da Muhimman Bayanai
  • Fasinjoji 4 sun rasu yayin da bas ta kama da wuta a Jigawa
  • Tawagar Iran A Majalisar Dinkin Duniya Ta Kare Matakin Sayar Da Jirgin Samanta Mara Mataki Ciki
  • PDP ta lashe zaɓen ƙananan hukumomin Osun
  • Gwamna Adeleke Ya Kaɗa Ƙuri’a a Zaɓen Ƙananan Hukumomin Osun
  • Turji Ya Ƙaƙaba Wa Ƙauyen Mataimakin Gwamnan Sokoto Da Wasu Biyan Harajin Miliyan 22