Leadership News Hausa:
2025-04-17@09:44:23 GMT

Kar A Ji Tsoron Aikace-Aikacen Kasar Amurka

Published: 24th, February 2025 GMT

Kar A Ji Tsoron Aikace-Aikacen Kasar Amurka

To, ma iya cewa kasar Amurka ta riga ta fusata dukkan kasashen duniya. Idan an sa wata kasar dake nahiyar Afirka fuskantar matakin da kasar Amurka ta dauka ita kadai, to, za ta ji akwai matsin lamba. Sai dai yanzu za a saki jiki, saboda ko da yake kasar Amurka ta kan ci zarafin sauran kasashe, amma ba ta da karfin cin zarafin dukkan kasashe a sa’i daya.

Wannan shi ne dalilin da ya sa ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya bayyana a wajen taron aikin tsaro na Munich da ya gudana a kwanan nan, cewa bai kamata a ji tsoron aikace-aikacen kasar da ta ke ta nuna fin karfi a duniya ba, saboda galibin kasashen duniya dake tsayawa kan adalci da hadin kai za su cimma nasara a karshe.

Ban da halartar taron tsaro a Munich a wannan karo, Wang Yi ya kuma shugabanci taron kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya, da halartar taron ministocin waje na rukunin kasashe 20 (G20), duk a kwanakin baya. Inda ya jaddada manufofin Sin na aiwatar da ra’ayin kasancewar bangarori masu fada-a-ji da yawa a duniya, da tsayawa kan daidaituwa, da adalci, da hadin kai, gami da neman zaman lafiya da ci gaban tattalin arziki, da hadin gwiwa don tabbatar da moriyar juna, da dai sauransu. Mahalarta tarukan sun nuna yabo kan jawaban ministan na kasar Sin, ganin yadda maganarsa ta kwantar da hankalinsu. Saboda ta nuna cewa, kasar Sin har kullum tana samar da tabbaci ga tsare-tsaren duniya, da ba da gudunmowa a kokarin tabbatar da ci gaban harkokin duniya.

Ban da haka, Wang Yi ya gana da takwaransa na kasar Angola, dake shugabantar kungiyar kasashen Afirka ta AU a karba-karba, Tete Antonio. Inda Wang ya ce, “‘Yan uwa Sinawa dake nahiyar Afirka sun san wace ce kawa ta gaske ta Afirka. “Wannan wata tsohuwar magana ce, amma yanzu ta nuna ma’ana mai zurfi.

Haka zalika, Wang ya ce, “A yunkurin kasashen Afirka na raya kai a nan gaba, kasar Sin za ta ci gaba da kokarin ba da taimako a matsayin wata sahihiyar abokiya.” Tabbas, za a iya tabbatar da makomar Afirka mai haske, bisa hadin kanta da kasar Sin, da huldar cude-ni-in-cude-ka dake tsakanin daukacin kasashe masu tasowa. (Bello Wang)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: kasar Amurka

এছাড়াও পড়ুন:

Al’ummar Babura Sun Karrama Sabon Shugaban Asibitin Koyarwa Na Rasheed Shekoni

Al’ummar Babura sun shirya gagarumin taron girmamawa domin karrama Dr. Salisu Mu’azu, bayan nada shi a matsayin Daraktan kuma babban likitan asibitin koyarwa na Rasheed Shekoni da ke jihar Jigawa, da kuma samun matsayin mamba na Cibiyar Kasa (mni).

Da yake jawabi a wajen taron, Shugaban Kwamitin Shirye-shirye, Rabiu Umar, ya bayyana cewa an gudanar da taron ne domin nuna godiya ga Allah da kuma murnar manyan nasarorin da Dr. Mu’azu ya samu.

Ya yaba da kokarin Daraktan wajen gudanar da aikinsa da kwarewa, da kuma ci gaba da tallafa wa al’umma.

A sakon da aka gabatar a madadin Mai Martaba Sarkin Ringim, Alhaji Dr. Sayyadi Abubakar Mahmoud, wanda Mai Girma Alhaji Usman Sayyadi, Babban Hakimin Masarautar, ya wakilta, ya nuna godiya ga masu shirya taron.

Ya bayyana karramawar a matsayin abin da ya dace da Dr. Mu’azu, yana mai jaddada jajircewarsa, da tausayi da himma wajen yi wa al’umma hidima.

Haka zalika, Shugaban Karamar Hukumar Babura, Alhaji Hamisu Muhammad Garu, ya taya Dr. Mu’azu murna bisa nasarorin da ya samu a fannin aikin likitanci, inda ya danganta hakan da jajircewa da  amana.

Ya tabbatar masa da cikakken goyon bayan al’umma tare da addu’ar samun karin nasarori.

A nasa bangaren, Dr. Salisu Mu’azu ya bayyana godiya sosai bisa girmamawa da karramawar da al’ummarsa ta masa.

Ya kuma nuna godiya ga Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Umar Namadi, bisa damar da ya ba shi zuwa makarantar NIPSS da ke jihar Filato.

A yayin taron, mutane da kungiyoyi daban-daban sun mika kyaututtuka da lambobin yabo ga Daraktan, ciki har da reshen kungiyar likitoci ta Najeriya na jihar Jigawa, J Health Beneficiaries, kungiyar Nas nas da Ungozoma ta kasa, da kuma kungiyar masu kula da lafiyar hakora ta Babura da sauransu.

 

Usman Muhammad Zaria 

 

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • MDD Ta Nuna Damuwarta Akan Kokarin Sake Raba Kasar Sudan Gida Biyu
  • Hadin Gwiwar Kasashen Asiya Da Afirka Na Habaka Karfinsu Na Dogaro Da Kai Da Cin Moriya Tare
  • Batawa Sin Suna Ba Zai Taimaka Kawar Da Tambarin Amurka A Matsayin Daular Kutsen Intanet Ba
  • Yaukaka Zumunci Da Makwabta A Aikace Tsakanin Sin Da Malaysiya
  • An Gudanar Da Taron Kasa da Kasa Don Tallafawa Yan Gudun Hijirar A Sudan
  • Za A Watsa Shirin Bidiyon “Bayanan Magabata Dake Jan Hankalin Xi Jinping” Na Harshen Malay
  • Firaministan Malaysia: Xi Jinping Babban Jagora Ne Mai Matukar Mayar Da Hankali Kan Abubuwan Dake Shafar Zaman Rayuwar Jama’a
  • Al’ummar Babura Sun Karrama Sabon Shugaban Asibitin Koyarwa Na Rasheed Shekoni
  • Amurka, Ki Fahimci Cewa “Girma Da Arziki Ke Sa A Ja Bajimin Sa Da Zaren Abawa”
  • Ministan Harkokin Noma Na Kasar Iran Ya Kama Hanya Zuwa Kasar Brazil