HausaTv:
2025-02-24@21:05:18 GMT

An Sanya Sayyid Safiyyuddeen Shahidi A Makwancinsa Ta Na Karshe A kudancin kasar

Published: 24th, February 2025 GMT

A yau Litinin ce aka sanya Sayyid Safiyyuddeen shugaban kungiyar Hizbullah wanda yayi shahada a hannun sojojin HKI a yakin Tufanul Aksa a makwanccinsa ta karshe a garinsu Deir-Qannoon Al-nahr dake kudancin kasar Lebanon.

Tashar talabijan ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta bayyana cewa dubban duruwan mutane ne suka halarci Jana’izar sa, sannan mutanen kauyuka a yankin da dama sun halarci jana’izar.

Mutane daga kasashen duniya da dama wadanda suka halarci jana’izar a jiya Lahadi a Beirt sun  halarci jana’izar Sayyid shahid Hashim safiyyudeen a yau a kudancin kasar ta Lebanon.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Al-Khazali: ‘Yan gwagwarmaya a Iraki za su gaba da bin tafarkin Sayyid Nasrallah

Dakarun gwagwarmaya a Iraki za su ci gaba da ayyuka bisa tafarkin babban sakataren kungiyar Hizbullah Sayyid Hasan Nasrallah, wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen kare wadanda ake zalunta, kamar yadda Qais al-Khazali, babban sakataren kungiyar Asa’ib Ahl al-Haq ya bayyana.

Da yake magana a ranar wannan Lahadin, al-Khazali ya jinjinawa Sayyed Nasrallah, yana mai bayyana shi a matsayin babban mutum wanda ya shafe tsawon rayuwarsa a tafarkin jihadi da kare wadanda ake zalunta.

Ya kara tabbatar da cewa babu makawa wa’adin Sayyed Nasrallah na samun nasara a kan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila yana zuwa.

“Mun yi alkawarin shrda ma Nasrallah cewa, za mu ci gaba da tafiya a kan wannan tafarki har zuwa lokacin da za a tsarkakae kasar Falastinu daga mamayar  gwamnatin Haramtacciyar kasar Isra’ila da yahudawan sahyuniya, in ji shi.

A cewar Hani Khater, shugaban ofishin yada labarai na Al-Ahed na kasar Iraki a ofishin Tehran, kimanin ‘yan kasar Iraki dubu 200 ne suka halarci jana’izar Sayyed Nasrallah a jiya Lahadi a birnin Beirut.

Sannan kuma Ya yi nuni da cewa, akidar Sayyed Nasrallah za ta ci gaba da dawwama a duk fadin yankin gabas ta tsakiya da ma duniya baki daya.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • IRGC Ta Bayyana Cewa Taron Jana’izar Nasarallah Ya Yi Tisara A Duniya Gaba Daya Saboda Barazanar Da Jiragen Yakin HKI Ta Yi Wa taron
  • Iran ta yi Allah wadai da keta hurumin kasar Lebanon da Isra’ila ta yi
  • Al-Khazali: ‘Yan gwagwarmaya a Iraki za su gaba da bin tafarkin Sayyid Nasrallah
  • Lebanon: An Rufe Shahid Sayyid Hassan Nasrallah A Makwancinsa Na Karshe A Birnin Beirut
  • Sharki: Takaitaccen Rayuwar Sayyid Shahid Hassan Nasarallah (r)
  • Wakilin Jagoran Juyi A Wurin Jana’izar Sayyid: Gwgawarmaya Za Ta Ci Gaba
  •  Sheikh Zakzaky:  Gwagwarmayar Musulunci A Lebanon Ta Sake Jaddada Kanta
  • Kungiyar Hizbullah Ta Lebanon Ta Jaddada Rashin Amincewarta Da Mika Kan Kasar Ga Amurka Da Haramtacciyar Kasar Isra’ila
  • Tawagogi Na Isa Lebanon Domin Halartar Jana’izar Sayyed Hassan Nasrallah