Gwamnatin Iraki Ta Kokawa Sabuwar Gwamnatin Siriya Dangane Da Barazanar Mayakan Daesh Da Suka Rage A Kasar
Published: 24th, February 2025 GMT
Shugaban hukumar Leken asiri na kasar Iraki Hamid al-Shatri ya bayyana cewa gwamnatin kasar Iraki ta isar da sako ga sabuwar gwamnatin kasar Siriya dangane da samuwar ragowar mayakan kungiyar yan ta’adda ta Daesh a wasu yankunan kasar.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta Nakalto Hamid al-Shatri ya na fadar haka ga kafafen yada labarai a birnin Bagdaza, sannan ya kara da cewa al-amuran tsaro a kasashen biyu suna hade juna ne, don haka dole ne gwamnatocin kasashen biyu su yi aiki tare don ganin bayan wadannan yan ta’adda, masu kafirta musulmi.
Kamfanin dillancin labaran INA na kasar Iraki ya nakalto al-Shatri yana fadar haka a taro na 7TH na tattaunawar Bagadaza a jiya Lahadi. Ya kara da cewa gwamnatin kasar Iraki ta maida hankali sosai kan yan ta’adda ta Daesh ne saboda yankunan hamadan mai yawa da ke da tsakanin kasashen biyu. Ta inda mai yuwa wasu daddaikun yayan kungiyar su sulale su shiga kasar ta Iraki.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: kasar Iraki
এছাড়াও পড়ুন:
Dangote ya karya farashin fetur karo na biyu a mako guda
Mako guda bayan rage farashin fetur da Naira 45, matatar mai ta Dangote ta sake karya farashin man ga ‘yan sari da ragin Naira 30 duk lita.
Aminiya ta rawaito cewa matatar na sayar da man ne a ranar Laraba akan ₦835, saɓanin makon da ya gabata da ta sayar da shi akan ₦865 bayan rage farashin daga ₦880 da ta sayar a makon da ya gabata.
Majalisa ta gayyaci Kantoman Ribas, Ibok-Ete Ibas An naɗa mace ta farko mai magana da yawun rundunar sojin NijeriyaHakan dai na nufin a cikin makonni shida, Dangoten ya rage farashin fetur ɗin sau uku.